Zaben jihar Bayelsa: Gwamna Dickson ya sayi rigunan Sojoji, yan sanda domin baiwa yan daba ranar zabe - APC

Zaben jihar Bayelsa: Gwamna Dickson ya sayi rigunan Sojoji, yan sanda domin baiwa yan daba ranar zabe - APC

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, tayi zargin cewa gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, da jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, sun sayi rigunan yan sanda da Soji na bogi.

Hakazalika an yi zargin cewa PDP ta kera katunan zabe na bogi domin kawo rikici zabe ranar 16 ga Nuwamba, 2019.

A wani jawabin da mataimakin kakakin APC, Yekini Nabena, ya tuhumci gwamna Seriake Dickson, da sakin wasu fursunoni 100 daga gidan yarin Okaka domin amfani da su lokacin zabe.

A cewarsa, gwamnatin jihar na shirin baiwa mutane dubu ashirin-ashirin a ranar zabe domin su zabi jam'iyyar PDP.

Mataimakin Kakakin APC na kasa ya ce banda binciken leken asirin da suka samu, wasu yan cikin gidan gwamnan sun bayyana yadda PDP ke shirin tafka magudi a ranar Asabar.

Yakini Nabena yace: "Wani mamban kwamitin yakin neman zaben PDP da aka nada kwanan nan ya yi murabus daga kwamitin kuma ya bayyana hakan gwamnan ke shirye-shiryen tafka magudi a zabe."

"Saboda haka, ina kira ga al'umma da jami'an tsaro bisa ga wannan jawabi da wani mamban kwmaitin yayi."

Ranar Asabar za'a tsageta tsakanin Sanata Duore Diri na jam'iyyar PDP da David Lyon na jam'iyyar a APC a jihar Bayelsa.

Yayinda gwamnan jihar ke goyon bayan Duoru Diri' ministan harkokin man fetur ke goyon bayan David Lyon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel