Da duminsa: An yi garkuwa da malaman jami'ar ABU da KADPOLY

Da duminsa: An yi garkuwa da malaman jami'ar ABU da KADPOLY

Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da malaman jami'a biyu a unguwar Mahuta a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Malaman masu suna Adamu Chinoko da Umar Chinoko yan'uwa ne kuma suna karantarwa a jami'ar Ahmadu Bello (ABU), Zaria, kuma dayan a a kwalejin KADPOLY.

A cewar rahotanni, an sace Adamu ne daren Alhamis inda masu garkuwa da mutanen suka tuntubi iyalin kuma suka bukaci kudin fansar milyan biyu da sabon babur.

Yayinda da uwansa Umar Chinoko, ya kai musu kudin ranar Lahadi, sai suka tsareshi.

An tuntubi Kakakin hukumar yan sandan jihar Kaduna, Yakubu Sabo, amma ba'a sameshi a waya ba.

DUBA NAN Gwamna Dickson ya sayi rigunan Sojoji, yan sanda domin baiwa yan daba ranar zabe - APC

Kasancewan yan jihar Kebbi ne, kakakin kungiyar yan jihar Kebbi mazauna Kaduna, Garva Mohammad, ya tabbatar da aukuwar hakan.

Yace: "Dakta Umar Chinoko ya je biyan kudin fansar milyan biyu da sabon babur din da suka bukata sai suka tsareshi,"

"Bayan sun karbi kudin sai suka ce sai an kara biyan kudin fansar milyan biyar. A yanzu da nike magana suna hannun masu garkuwan."

A wani labarin mai kama da haka, masu garkuwa da mutane sun addabi unguwar Rigasa dake karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Mazauna unguwar sun kai zanga-zanga majalisar dokokin jihar kan yadda ta'addancin ya zama ruwan dare a unguwar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel