Bayan mahaifi ya mika yaronsa ga yansanda a Kano, sun kasheshi da duka

Bayan mahaifi ya mika yaronsa ga yansanda a Kano, sun kasheshi da duka

Jami'an yan sanda a jihar Kano sun lallasa wani matashi mai suna, AbdulKadir Nasiru, har lahira bayan mahaifinsa ya mikashi ga yan sandan don gudanar da bincike bayan sun zargeshi da aikata laifi.

Daily Nigerian ta bada rahoton cewa mahaifin AbdulKadir ya mika dansa ya ofishin yan sanda dake Madobi a jihar Kano bayan sun alanta nemansa ruwa a jallo kan rikicin da sukayi a unguwa.

Mahaifin ya bayyanawa manema labarai cewa a matsayinsa da uba na kwarai kuma mai bin doka, ya mika dansa ga hukuma domin gudanar da bincike.

"Kawai sai daya daga cikin yan sandan ya fara dukansa a gabana bayan wani mujadala da suka samu. Sai wani dan sandan ya shiga fadan yana dukansa, shi kuma yana ramawa."

"Ganin yadda na ga suna dukansa kawai na fita daga ofishin hukumar saboda ba zan iya zuba ido ana dukan yarona kan abin da bai taka kara ya karya ba."

Cikin hawaye, mahaifin ya ce da ya isa gida, sai ya tura yayan AbdulKadir ya je ya baiwa yan sandan hakuri.

Amma yayan mai suna, Ahmed Nasir, ya ce yan sandan basu saurareshi ba yayinda suke cigaba da dukansa har ya fadi warwas kumfa na fitowa daga bakinsa.

Yace sai da ya biya yan sanda N8,000 kafin suka barshi ya kai kaninsa asibiti inda likitoci suka bayyana cewa ya riga ya cika.

Iyalinsa sun mika kokon bararsu ga gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, da kwamishanan yan sanda su tabbatar da cewa an hukunta wadanda suka aikata wannan.

Kakakin hukumar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da cewa zuwa yanzu an damke yan sanda hudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel