Har yanzu ni ne gwamna - Gwamnan PDP da kotu tace an tafka magudi a zabensa

Har yanzu ni ne gwamna - Gwamnan PDP da kotu tace an tafka magudi a zabensa

Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo, yayi kira ga magoya bayansa da ke fadin kasar nan da su kwantar da hankalinsu saboda har yanzu shine gwamnan jihar.

Yayin mayar da martani akan zaman kotun da aka yi yau, Makinde yace har yanzu ba a yanke wani hukunci da ya saukesa daga kujerarsa ba.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta yanke hukuncin cewa Seyi Makinde na jam'iyyar PDP ne ya lashe zaben gwamnan jihar Oyo wanda suka kara da Adebayo Adelabu na jam'iyyar APC.

Adebayo ya kalubalanci hakan a kotun sauraron kararrakin zabe inda ya mika bukatar soke wannan nasarar ta Makinde tare da bada umarnin yin sabon zabe amma kotun ta soke bukatarsa.

Muhammad Surajo, shugaban alkalan kotun, ya ce wannan kara ba abun dogaro bace.

DUBA WANNAN: Ba na maraba da karuwai a masarauta ta - Babban Sarki a arewa

Amma kuma Adelabu ya garzaya zuwa kotun daukaka kara wacce a yau Litini ta ce Makinde bai samu halastattun kuri'u masu rinjaye ba da zasu bashi nasarar zaben. Tace an saka kuri'u fiye da mutanen da aka tantance kuma an taka dokokin da zabe ya tanadar.

Amma kuma kotun bata kwace kujerar gwamnan ba kuma bata umarci da ayi sabon zabe ba.

Saidai, sanarwar tayi matukar tasiri a zukatan magoya bayan Adelabu wanda har murna da jindadi ya kaure tsakaninsu. A hakan ne kuma aka bada rahoton Adelabu Adebayo na jam'iyyar APc ne ya lashe zaben.

A yayin maida martani ga wannan cigaba, Makinde ya zargi jam'iyyar adawar da yaudarar mutane.

"Akwai rashin tunani ga duk wanda zai yi fatan wannan nasarar zata kufce. Duk da zasu yi fatan faruwar hakan, amma ba zata faru ba. Mutanen jihar Oyo ne suka zabeni," in ji shi.

Ya kara da cewa, "Babu wani abun damuwa saboda duk abinda 'yan adawa ke kullawa ya fallasu. Ma'aikatar shari'a na da kwarewa kuma bazata bari ayi amfani da ita ba wajen tozarta mutanen jihar Oyo,"

"Ina kira ga mutane da su cigaba da harkokinsu, hankalinmu ba zai dauke ba wajen yi wa mutanen jihar aiyukan alheri ba. Gwamnati ta gari tare da shugabanci nagari ne ya dace da ku." in ji Makinde.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel