Sunayen kwamishinon 'yan sanda 13 da suka samu karin girma zuwa AIG

Sunayen kwamishinon 'yan sanda 13 da suka samu karin girma zuwa AIG

Babban sifeton rundunar 'yan sanda na kasa (AIG), Mohammed Adamu, ya bayar da umarnin yin sauyin wurin aiki ga wasu kwamishinonin 'yan sanda 13 da ya bayar da umarni a kara musu mukami zuwa mataimakansa.

An sanarwar da rundunar 'yan sanda ta fitar, sauyin wurin aikin da aka yi wa sabbin AIGs din ya fara aiki nan taki.

AIG Adamu ya bukaci sabbin mataimakan nasa da su yi amfani da gogewarsu ta aiki domin taimaka wa rundunar 'yan sanda ta cimma muradunta.

Kazalika, ya umarci su saka ido sosai a bangarorin da aka nada su jagoranta domin kawo canji a salon aikin rundunar 'yan sanda.

Sabbin mataimakan 13 da wurin aikinsu sune kamar haka;

1. AIG Dan Bature, fdc – Mataimakin sifeton rundunar 'yan sanda DFA FHQ

2. AIG Hyelasinda Kimo Musa – Mataimakin sifeton rundunar 'yan sanda PMF

3. AIG Yunana Y. Babas, mni– Mataimakin sifeton rundunar 'yan sanda mai kula da shiyyar 'yan sanda ta 8 da ke Lokoja

4. AIG Dan Mallam Mohammed, fdc – Mataimakin sifeton rundunar 'yan sanda SPU

5. AIG Mua’zu Zubairu Halilu – Mataimakin sifeton rundunar 'yan sanda CTU

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Rundunar soji ta kara wa manyan sojoji fiye da 34 girma zuwa mukamin manjo janar

6. AIG Rabiu Yusuf – Mataimakin sifeton rundunar 'yan sanda a bangaren ICT

7. AIG Ahmed Iliyasu – Mataimakin sifeton rundunar 'yan sanda a shiyya ta 2, Lagos

8. AIG Mohammed Uba Kura – Mataimakin sifeton rundunar 'yan sanda a bangaren 'yan sandan ruwa (Maritime)

9. AIG Zaki M. Ahmed – Mataimakin sifeton rundunar 'yan sanda a shiyya ta 6, Calabar

10. AIG Zama Bala Senchi – Mataimakin sifeton rundunar 'yan sanda a bangare 'Community Policing'

11. AIG Bello A. Sadiq – Mataimakin sifeton rundunar 'yan sanda a shiyya da 1, Kano

12. AIG Austin Agbonlahor Iwero, fdc – Mataimakin sifeton rundunar 'yan sanda DOPS FHQ

13. AIG Lawal Ado – Mataimakin sifeton rundunar 'yan sanda a bangaren aiyuka (Works)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel