Bai halatta Jihohin da ke Shari’a su karbi kason harajin giya ba Inji Malamin Jami'a

Bai halatta Jihohin da ke Shari’a su karbi kason harajin giya ba Inji Malamin Jami'a

Wani Malamin ilmin musulunci a jami’ar Al-Hikmah da ke Ilorin a jihar Kwara, Sanusi Lafiagi, ya yi wata hira da ‘Yan jarida kwanaki, inda ya tattauna a kan wasu batutuwa da su ka shafi Najeriya.

Mun tsakuro wasu bangare daga cikin wannan tattaunawa da ‘yan jarida su ka yi da Malamin.

Shan giya a Musulunci da aikin Hisbah wajen rusa kwalaben giya

Musulunci ya haramta amfani da duk wani abu mai sa maye, ko giya ne, ko ba giya ba ne. Domin ya sabawa manyan kudirorin musulunci na kare rayuka, addini, hankali, dukiya da martaba.

A cikin Sura ta 5: Aya ta 90 da wasu Hadisan Manzon Allah SAW, an tabbatar da cewa shan kayan maye haramun ne, haka zalika cinikinsu, da kuma hadasu, da dakonsu da kuma mikawa wani su.

A game da jami’an hukumar Hisbah da ke fasa kwalaben giya a Jihohin shari’a, Malamin ya ce a na sa tunani Hisbah ta na da hurumin yin hakan a dokar kasa a wadannan jihohin da aka kafa ta.

Idan har cikin aikin ta akwai lalata kwalaben giya, shi kenan ya yi daidai. Ya kamata a san cewa inda ake wadannan aiki, wurare ne da ake dabbaka shari’a saboda rinjaye al’ummar Musulmai.

KU KARANTA: Abin da ya sa Musulmai su ke yin Mauludin Annabi - Dahiru Bauchi

Daidai ne Jihohin da ke aiki da shari’a su rika karbar kasonsu na harajin kayan giya?

A’a, ba daidai ba ne a gare su, su raba abin da aka karba na kayan haram. Wannan zai zama tafka da warwara a Musulunci. Addini ya hana shan giya da cin ribar cinikin duk wani kayan haram.

Almajiranci addini ne?

Kalmar almajiri a iya sani na ta na nufin ‘Dan ci-rani mai hijira. An dauko ta ne daga kalmar Al-Muhajir. Ma’ana mai tashi daga wani wuri zuwa wani. Don haka aka san almajirai da barin Garuruwansu domin samun ilmin addini a gaban Malamai da su dauki duk wata dawainiyarsu.

Malamin addinin ya ce duk da irin ribar da aka ci da wannan tsari, yanzu sha’anin ya tabarbare, tsarin ya zama wani abu dabam da ya zama musiba a cikin al’umma. Ya ce ba a daukar nauyin yaran kuma babu ruhin addini, sai dai yawan bara don haka ya bukaci ayi wa tsarin garambawul.

Tasirin Almajiranci ya na da karfi matuka. Rikicin Boko Haram, satar jama'a, bakin jahilici da talauci duk su na cikin tasirinsa a addini da kasarmu, an kai ana juya kansu, ana amfani da su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel