Ba na maraba da karuwai a masarauta ta - Babban Sarki a arewa

Ba na maraba da karuwai a masarauta ta - Babban Sarki a arewa

Shehun Bama na jihar Barno, Kyari Ibn Umar El-Kanemi, ya bayyana cewa, ba a maraba da karuwai a yankinsa saboda gujewa aukuwar munanan lamurra tare da wanzar da zaman lafiya a yankin.

Abba Shehu-Umar, sakatare na musamman, a takardar da ya fitar ranar Litinin a garin Maiduguri, ya ce, sarkin ya yi wannan bayanin ne a sakon da ya mika ga jama'arsa a ranar Lahadi yayin bikin murnar maulidin manzo, Annabi Muhammadu SAW.

Yace, sarkin ya nuna rashin jin dadinsa akan yadda yawan karuwai ke kara hauhawa a yankin.

Kamar yadda El-Kanemi ya ce, an samu yawaitar lamurran ashsha a yankin tun bayan da 'yam matan' suka dawo yankin.

Basaraken ya ce, masarautarsa bazata aminta da irin wannan dabi'ar ba ko kuma duk wani aikin ta'addanci da ake zargin karuwan da aikatawa.

DUBA WANNAN: Dangote ya nada 'yarsa a matsayin daya daga cikin manyan daraktocinsa

"Idan zaku tuna, wadannan yam matan sun jawo tashin hankula masu yawa a babban birnin jihar. Sun fada harkar karuwanci, safarar yara, shaye-shaye da sauran aiyukan ashsha a tsakar jihar,"

"Gwamnatin jihar ta kafa karfafan kwamiti don shawo kan wadannan lamurran. An kuwa fara hakan ne ta hanyar rushe manyan otal, gidan karuwai da sauran maboyarsu a Maiduguri. Yanzu basu da kasuwa a babban birnin jihar wanda hakan yasa suke komawa wasu kananan hukumomin jihar."

"Wannan ba abinda zamu zuba ido mu kalla bane; Na umarci dagatai da masu unguwanni da su zuba ido tare da hana irin wannan harka a yankinsu," in ji El-Kanemi.

Sarkin yace duk wadanda aka kama da irin wadannan laifuka, za a gurfanar dasu kuma za a cigaba da rushe duk maboyarsu kamar yadda dokar gwamnatin ta gindaya a Maiduguri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel