Dangote ya nada 'yarsa a matsayin daya daga cikin manyan daraktocinsa

Dangote ya nada 'yarsa a matsayin daya daga cikin manyan daraktocinsa

An nada Halima Dangote a matsayin daya daga cikin babbar daraktar kamfanin. Kamar yadda kamfanin ya sanar, Halima Aliko Dangote zata koma kamfanin ne bayan da tayi aiki a bangarori biyu na kasuwancin kamfanin a shekaru biyar da suka gabata.

Tana daya daga cikin jigo a fannin kudi na gidauniyar tallafin Dangoten. A cikin kwanakin nan ne Halima ta sauka daga daraktar kamfanin fulawa ta kamfanin.

Ta rike matsayin babbar daraktar NASCON, masu samar da gishiri, kayan dandano da sauransu wadanda ke da matukar kasuwa wajen ma'abota amfani dasu.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Rundunar soji ta kara wa manyan sojoji fiye da 34 girma zuwa mukamin manjo janar 32

Halima ce shugabar Board of The Africa Center da ke New York, wata cibiya ce ta musamman da ke hada kasuwanci, dokoki da al'adun Afirka. Jigo ce a Endeavour Nigeria kuma mamba ce a Women Corporate Directors. Tana da gogewar aiki na sama da shekaru 12.

A sabon matsayinta, kula da tabbatar da cigaba ga dokokin masu ma'amala da kamfanin Dangote ya rataya a kanta. Zata kula da tabbatar da dabarun hangen nesa a bangarori da dama na kamfanin.

Halima na da ra'ayi a bangaren kawo cigaba ga mata. Tana da digiri na farko a fannin kasuwanci a American Intercontinental University da ke Landan da kuma digiri na biyu a fannin kasuwanci daga makarantar kasuwanci ta Webster da ke UK.

Ta halarci manyan shirye-shirye na cigaba da habaka kasuwanci a manyan jami'o'in duniya

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel