Bayero sun hadu da Iwuanyanwu da wasu domin kawo karshen satar yaran Arewa

Bayero sun hadu da Iwuanyanwu da wasu domin kawo karshen satar yaran Arewa

- Mai martaba Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero ya kai ziyara zuwa kasar Kudu

- Sabon Sarkin ya gana da manyan kasar Ibo ne a kan sace yara da ake yi a Kano

- Emmanuel Iwuanyanwu ya yaba da halin Shugaba Buhari a zaman da su ka yi

Mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero ya tashi daga kasar Kano zuwa Kudu maso Gabashin Najeriya a game da matsalar satar kananan yaran da ake fama da ita a jihar Kano.

Kamar yadda mu ka samu labari, Sarkin ya fara wannan ziyara ne tun Ranar Alhamis, 7 ga Watan Nuwamba, inda ya ziyarci gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, da kuma jami’an tsaro.

Daga nan Mai martaban ya zarce jihar Imo, ya samu zantawa da Emeka Ihedioha. Wannan ziyarar sabon Sarkin ta kai sa har gaban Dattawan na kasar Ibo irinsu Cif Emmanuel Iwuanyanwu.

Emmanuel Iwuanyanwu ya karbi bakuncin Sarkin na Bichi da Tawagarsa ne a gidansa da ke babban birnin jihar Imo na Owerri a Ranar Lahadi kamar yadda Jaridar The Nation ta rahoto.

KU KARANTA: Wani Hadimin Ganduje ya kira Sarki Sanusi mai kazamin baki

Iwuanyanwu ya yi wa Sarkin karin haske kan kokarin da ake yi na nunawa Duniya mutanen Ibo ba su son shugaban kasa Muhammadu Buhari, Cif Iwuanyanwu ya ce hakan ba gaskiya ba ne.

A cewar Iwuanyanwu, abin da mutanen kasar Kudu maso Gabashin Najeriyar su ke so shi ne a rika yi wa kowa adalci a kasar. Dattijon ya yabawa shugaban kasa Muhamadu Buhari a zaman.

The Nation ta rahoto Dattijon na kasar Ibo ya na yabon halin shugaban kasa Buhari na gaskiya da rikon amana. Emmanuel Iwuanyanwu ya ce Buhari mutum ne da bai da kashin rashin gaskiya.

Satar yaran da ake yi a Arewa ya zama ruwan dare, don haka Sarki Aminu Ado Bayero ya nemi ya zauna da mutanen Kudu maso Gabashin kasar da nufin ganin an daina wannan danyen aiki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel