Yanzu Yanzu: APC ta yi gagarumar nasara yayinda kotun daukaka kara ta soke zaben gwamnan Oyo

Yanzu Yanzu: APC ta yi gagarumar nasara yayinda kotun daukaka kara ta soke zaben gwamnan Oyo

- An shiga rudani kan sabon matsayin gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde

- Kotun daukaka kara a ranar Litinin, 11 ga watan Nuwamba ta yanke hukunci inda Adelabu na APC ya yi nasara a karar da ya shigar sannan ta janye hukuncin kotun zabe wacce ta kaddamar da Makinde a matsayin ainahin wanda ya lashe zabe

- Sai dai kuma kotun zaben ba ta kaddamar da tsige Makinde ko umurnin sake sanon zabe ba

Kotun daukaka kara da ke zama a Ibadan, babbar birnin jihar Oyo ta soke zaben Gwamna Seyi Makinde na jihar.

A cewar jaridar Daily Nigerian, kotun ta yanke hukunci ne a karar da Adelabu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya daukaka.

Kotun ta dage hukuncin kotun sauraron karar zabe wacce ta jaddada nasarar Makinde. Sai dai kuma, kotun ba ta kaddamar da Adelabu a matsayin wanda ya yi nasara ba.

Kotun ba ta kuma yi umurnin sake sabon zabe ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Hankula sun tashi a Kogi yayinda yan iska suka kona sakatariyar jam’iyyar SDP yan kwanaki kafin zabe

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Seyi Makinde ya bayyana cewa ya kwashe tsawon shekara 13 na rayuwarsa wajen siyar da biredi a bakin asibitin Adeoyo a Ibadan, kafin ya zama Gwamnan jihar Oyo.

Gwamnan na jihar Oyo ya bayyana hakan ne a wajen bikin cikar mahaifiyarsa, Misis Abigael Makinde shekara 80 wanda aka gudanar a cocin St Paul Anglican Church da ke Yemetu a ranar Lahadi, 10 ga watan Nuwamba, cewa ya zama wani mai fada a ji ne ta hanya samun ilimi.

A cewarsa, ya kaddamar da ilimi kyauta a jihar ne domin ganin cewa mazauna jihar sun amfana wajen samun ingantaccen ilimi. Gwamna Makinde ya kuma bukaci iyaye a jihar da su dauki karatun yaransu sama da komai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel