Hadimin Gwamna Ganduje ya caccaki sarki Sanusi

Hadimin Gwamna Ganduje ya caccaki sarki Sanusi

- Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, ya sha caccaka daga wajen hadimin gwamna Ganduje na jihar Kano

- Hadimin gwamnan, Salihu Tanko Yakasai, bai ji dadin furucin da Sarki Sanusi ya yi ba a kan yaran da aka ceto kwanan nan daga hannun masu safarar mutane

- Yakasai, wanda aka fi sani da Dawisu, ya ce furucin basaraken na cike da rashin tunani

Wani hadimin Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Gaduje, Salihu Tanko Yakasai, wanda aka fi sani da Dawisu, ya haifar da rudani a kafar sadarwa bayan ya zargi Sarki Sanusi Lamido Sanusi da fadin shirme.

Legit.ng ta tattaro cewa Yakasai ya yi furucin ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Nuwamba a shafinsa na Twitter, @Dawisu, a martaninsa game da furuci da babban basaraken arewan ya yi kan sace yara da wasu masu safarar mutane suka yi kwanan nan a Kano.

A rubutun farko da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Dawisu ya ce Sarki Sanusi ya yi shiru da kazamin bakinsa kan shawarar da ya bayar na cewa kamata ya yi a kama iyayen yaran da aka sace a kan rashin kulawa.

Hadimin Gwamna Ganduje ya caccaki sarki Sanusi

Hadimin Gwamna Ganduje ya caccaki sarki Sanusi
Source: Twitter

Sai ya kara wallafa wani rubutu inda a ciki ya caccaki jigon addinin kan shiru da ya yi kan lamarin na tsawon lokaci, sai kuma kawai ga shi yaa fadin wani Magana mara ma’ana ga iyayen yara.

Ya kuma cigaba da zargin sarkin da rashin tabuka abun kirki a rayuwar talakawansa.

Idan za ku tuna a kwanakin baya ne dai Salihu Tanko Yakasai ya kira ruwa da wata kasassaba daya tafka a shafin kafar sadarwar zamani ta Twitter, inda ya yi ma mataimakin shugaban kasa Osinbajo shagube.

Jaridar Punch ta ruwaito Yakasai ya bayyana mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne a matsayin ‘Mataimakin shugaban kasa mai kula da al’amarin karatu’ ta shafinsa mai adireshi @dawisu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel