Cikin watanni 9, Kwastam ta samu tiriliyan 1 na kudin shiga

Cikin watanni 9, Kwastam ta samu tiriliyan 1 na kudin shiga

Hukumar hana fasa kwabrin Najeriya wato Kwastam ta samarwa Najeriya kudin shiga na kimanin N1.002 trillion daga watan Junairu zuwa Satumban 2019.

Bisa ga sashen bincike da lissafin hukumar, kakakin hukumar ya bayyana cewa an samu wadannan kudade ne daga rassan hukumar 32 dake fadin tarayya.

Wannan lissafi na nuna cewa hukumar ta samu kudin shiga mafi yawa a watan July na N123.6 billion , sannan watar Mayu, N118.6 billion.

Hakazalika watan da aka samu mafi karanci shine watan Febrairu inda aka samu N86.3 billion.

Ana kyautata zaton cewa rufe iyakokin da akayi lokacin zaben 2019 ne ya sabbaba karancin da aka samu a watan Febrairu.

A cewar binciken, sashen Apapa a jihar Legas ce ta samar da kudi mafi yawa na N313.5 billion cikin watanni tara.

Bugu da kari, lissafin ya bayyana cewa rufe iyakokin Najeriya da gwamnatin tarayya tayi ya taimaka wajen karuwar kudin shiga saboda a watan Satumba, an samu N115.6 billion, fiye da abinda aka samu a Agusta.

Wannan na nuna cewa zuwa karshen shekara, hukumar za ta kece tarihin da ta kafa a shekarar 2018 da aka samu N1.2 trillion.

DUBA NAN Bidiyo ya bayyana matasan PDP suna lalata fostocin APC a Kogi, Dino Melaye yayi zagi a kasuwa

A wani labarin kuma, Ma'aikatar lura da arzikin man fetur wato DPR ta daina bada daman gina gida mai tare da janye bada lasisi ga gidajen mai dake da kusancin kilomita 20 da iyakokin Najeriya har lokacin da Allah yaso.

Jaridar Daily Trust ta bada rahoton cewa hukumar ta alanta hakan ga masu bukatar gina sabbin gidajen mai a yankunan.

DPR ta bayyana cewa dalilin da yasa ta yanke wannan shawara shine taimakawa muradun gwamnati na hana fasa kwabrin man fetur a iyakokin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel