Kalaman Sarki Sanusi II: An sako hadimin Ganduje a gaba a kan mayar da martani

Kalaman Sarki Sanusi II: An sako hadimin Ganduje a gaba a kan mayar da martani

An caccaki Salisu Yakasai, wani hadimin Gwamnan jihar Kano a kafafen sada zumunta akan martanin rashin ladabi da ya maidawa Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II.

Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu, a ranar Lahadi ya je shafinsa na tuwita inda ya bukaci Sarki Sanusi Lamido da ya rufe bakinsa akan tsokacin da yayi akan yaran da ake sace daga jihar Kano aka sayar dasu a jihar Anambra. Sarkin ya bukaci a daure iyayen akan rikon sakainar kashin da suka yi wa 'ya'yansu.

A ranar Lahadi, Sanusi yace bai dace a ga laifin 'yan kabilar Igbo din ba, a maimakon haka a ga laifin iyayen yaran. Ya jaddada cewa, iyayen arewa na da dabi'ar barin 'ya'yansu suna zaga gari don bara, hakan ce ta ba masu satar yaran damar sacesu.

A yayin mayar da martanin, Yakasai wanda shine shugaban yada labarai da sadarwa ga gwamnatin jihar Kano, ya bukaci sarkin da ya rufe bakinsa.

Ya ce: "Wannan tsokacin na nuna rashin damuwa ne. Da kyar idan aka sace dan'uwansa ko aka yi garkuwa dashi zai iya wannan tsokacin. Yaran da aka sace ba almajirai bane. Yafi dacewa Sarki Sanusi Lamido ya rufe bakinsa a maimakon wannan maganar tashi. Rashin hankali!"

DUBA WANNAN: Daukaka guda da marigayi Murtala ne kawai ya samu a cikin tsoffin shugabannini mulkin soji Najeriya

Ya kara da cewa, "Bayan makonni da aukuwar lamarin, Sarkin bai fito ya jinjinawa jami'an tsaron kasar nan ba ta yadda suka zakulo wadanda ake zargin, kawai sai ya dau laifi ya dorawa iyayen yaran. Wannan rashin damuwa da me tayi kama?"

Tuni ma'abota amfani da kafar yada zumuntan ta tuwita suka yi caa akan Yakasai tare da taka masa birki.

Adamu Sarki Aliyu ya mayar da martani kamar haka: "Mai martabarmu yana kan hanya. Ya fadi gaskiya. Kada ka sanya siyasa cikin maganarsa."

Lamido kuwa cewa yayi, "Dawisu ya fadi tuni. Bansan me yasa yake fushi da Muhammad Sanusi ba."

AbdulMumeen Abdullah cewa yayi, "Ina tunanin akwai wani abu tsakaninka da sarkin. Wannan yafi karfin zama hadimin gwamnan. Zata iya yuwuwa Sarkin bai yi daidai ba amma cewa ya rufe bakinsa ba daidai bane. Kowa ya tsaya a matsayinsa."

AY_Zarewa kuwa yace: "Dawisu na ta maganganu a tuwita akan maganar Sanusi Lamido, ina 'yayansa suke idan karfe 10 na dare tayi? Yana barinsu ne gantali a titi? Jeka Yakasai karfe 10:30 na dare, zaka ga halin rashin ko in kula. Hakan ne ke taimakawa wajen safarar yara da fyade, ko kana so ko baka so."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel