Gwamnatin tarayya ta nuna damuwa kan yawan barkewar gobara a kasuwannin kasar

Gwamnatin tarayya ta nuna damuwa kan yawan barkewar gobara a kasuwannin kasar

- Gwamnatin tarayya ta nuna damuwa matuka akan yawan afkuwar gobara da ake samu a kasuwanni da ke fadin kasar

- Ministar taimakon jama'a da kiyaye afkuwar annoba, Hajiya Sadiya Umar Farouq ta bayyana hakan yayinda ta ke jaje ga wadanda suka rasa dukiyoyi da kayayyakinsu na miliyoyin naira a yayinda gobara ta barke a wasu yankuna na kasuwannin Balogun da Dosunmu a jihar Lagas a kwanan nan

- Ta ce ta yi bakin ciki matuka akan wannan lamari inda ta bayyana shi a matsayin babban asara ga jihar Lagas da kasa baki daya

Ministar taimakon jama'a da kiyaye afkuwar annoba, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta nuna damuwa matuka akan yawan afkuwar gobara da ake samu a kasuwanni da ke fadin kasar.

Ministar ta bayyana cewa yawan barkewar gobara da ake samu a yan kwanakin nan na matukar damun gwamnatin tarayya.

Ta bayyana hakan ne yayinda ta ke jaje ga wadanda suka rasa dukiyoyi da kayayyakinsu na miliyoyin naira a yayinda gobara ta barke a wasu yankuna na kasuwannin Balogun da Dosunmu a jihar Lagas a kwanan nan.

Ministar, a wani jawabi, ta ce ta yi bakin ciki matuka akan wannan lamari inda ta bayyana shi a matsayin babban asara ga jihar Lagas da kasa baki daya.

KU KARANTA KUMA: Wata kungiya ta yiwa Falana wankin babban bargo kan zargin da ya yiwa Buhari

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, Sadiya Umar Farouq, ta dora alhakin rashin karewar rikicin Boko Haram a kan rashin kyawawan dabaru da kulla alaka mai kyau bangaren rundunar soji da sauran kungiyoyi masu zaman kansu da ke yankin arewa maso gabas.

Uwargida Sadiya ta bayyana hakan ne a wurin bude wani taro na kwanaki uku na hadin gwuiwa da jami'an tsaro da aka fara a ranar Alhamis a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel