Bidiyo ya bayyana matasan PDP suna lalata fostocin APC a Kogi, Dino Melaye yayi zagi a kasuwa

Bidiyo ya bayyana matasan PDP suna lalata fostocin APC a Kogi, Dino Melaye yayi zagi a kasuwa

An ga wasu matasa na lalata hotunan yakin neman zaben gwamnan jihar Kogi, kuma dan takarar jam'iyyar All Progressive Congress (APC) Yahaya Bello, a babbar birnin jihar, Lokoja.

A wani bidiyo da ya bayyana, an ga wasu matasa suna lalata fostocin dake dauke da hoton gwamnan da mataimakinsa, Edward Onoja.

Hakazalika, yar takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), Natasha Akpoti, ya zargi gwamnan da laifin tura matasa lalata ofishin kamfenta.

Dan takarar kujerar Sanata a Kogi ta yamma ya yi tsokaci kan lamarin inda yayi zagi a kasuwa kan wadanda ke shirin yin magudin zabe.

Dino yace: "Wadanda ke canza sakamakon zabe su kalli wannan kuma su gargadi kansu."

Za'a gudanar da zaben gwamnan jihar Kogi ranar Asabar, 16 ga Nuwamba, 2019.

Kalli bidiyon:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel