Na shafe tsawon shekara 13 ina siyar da biredi – Gwamna

Na shafe tsawon shekara 13 ina siyar da biredi – Gwamna

- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa ya kwashe tsawon shekara 13 na rayuwarsa wajen siyar da biredi a bakin asibitin Adeoyo a Ibadan

- Makinde ya bayyana cewa wannan ne dalilin da ya sa ya kaddamar da ilimi kyauta a jihar domin kowa ya amfana daga moriyar da ke tattare da samun ingantaccen ilimi

- Ya bukaci iyaye da su sanya ilimin yaransu sama da komai, domin cewa ya zama wani mai fada a ji ne ta hanya samun ilimi

Seyi Makinde ya bayyana cewa ya kwashe tsawon shekara 13 na rayuwarsa wajen siyar da biredi a bakin asibitin Adeoyo a Ibadan, kafin ya zama Gwamnan jihar Oyo.

Gwamnan na jihar Oyo ya bayyana hakan ne a wajen bikin cikar mahaifiyarsa, Misis Abigael Makinde shekara 80 wanda aka gudanar a cocin St Paul Anglican Church da ke Yemetu a ranar Lahadi, 10 ga watan Nuwamba, cewa ya zama wani mai fada a ji ne ta hanya samun ilimi.

A cewarsa, ya kaddamar da ilimi kyauta a jihar ne domin ganin cewa mazauna jihar sun amfana wajen samun ingantaccen ilimi. Gwamna Makinde ya kuma bukaci iyaye a jihar da su dauki karatun yaransu sama da komai.

“A farkon shekaru 13 na rayuwana, inda muka zauna mai wuce mintina biyar daga inda muke ba a yanzu. Mahaifiyata ta kasance mai kula da talho a sakatariyar jihar. A asibitin Adeoyo na jihar anan ne ni da dan’uwana Muyiwa muke taya ta siyar da biredi a bakin kofar asibitin.

KU KARANTA KUMA: Wata kungiya ta yiwa Falana wankin babban bargo kan zargin da ya yiwa Buhar

“Ilimi ne kadai abunda zai sa wani yaro da ke zama a wasu yan mintina kadan daga Yemetu ya zama gwamnan jihar Oyo. Kuma wannan ne dalilin da yasa na kaddamar da ilimi kyauta a jihar Oyo,” in ji Makinde.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel