An fadawa Buhari ya yi watsi da kiran da ake yi na sauke Godswill Akpabio

An fadawa Buhari ya yi watsi da kiran da ake yi na sauke Godswill Akpabio

Wasu gungun tsofaffin Tsagerun Neja-Delta da ke jihar Akwa Ibom sun nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi fatali da kiran da ake yi masa na tsige Ministansa Godswill Akpabio.

Kungiyar Tsagerun da su ka tuba su ka kuma amfana da tsarin afuwar gwamnatin tarayya sun ma yabawa shugaban kasar ne a kan nada Godswill Akpabio da ya yi a matsayin Ministan yankin.

A cewar wannan kungiya, shugaban kasar bai yi zaben tumun dare ba wajen dauko tsohon gwamnan na Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio ya ba shi kujerar Ministan harkar Neja-Delta.

Hakan na zuwa ne bayan da wasu su ka fara kira a sauke Akpabio daga kan kujerarsa a sakamakon binciken da ake yi a hukumar NDDC wanda wannan zai bankado wasu kura a yankin.

Tsofaffin Tsagerun, a wani jawabi da su ka fitar ta bakin shugabansu, Imoh Okoko sun wanke Ministan daga zargin da ake yi masa na yin kutun-kutun wajen dawo da NDDC a karkashinsa.

KU KARANTA: ‘Dan Majalisar ya lissafo amfanin rufe iyakan da Shugaba Buhari ya yi

Kwamred Imoh Okoko ya bayyana cewa matakin da gwamnati ta dauka na dauke NDDC daga karkashin ofishin Sakataren gwammnati zuwa ma’aikatar Neja-Delta sam ba aikin Akpabio ba ne.

Okoko ya kuma kara da cewa babu hannun Ministan na Neja-Delta wajen kafa kwamitin mutum uku domin a binciki aikin da hukumar NDDC mai kula da cigaban Neja-Delta ta yi duk a baya.

Tsagerun sun fadawa kowa cewa ba za su bari a taba Ministan ba inda su ka zargi koke-koken da ake yi na tsigesa da cewa ya na da kanshin kabilanci da kuma son kai a yankin mai arzikin fetur.

A jawabin kungiyar, ta ce, Fasto Usani Usani ne ya fara rantsar da Nsima Ekere a NDDC, sannan kuma shugaban kasa da kansa ya bukaci a yi masa cikakken bincike a game da sha’anin NDDC.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel