Wata kungiya ta yiwa Falana wankin babban bargo kan zargin da ya yiwa Buhari

Wata kungiya ta yiwa Falana wankin babban bargo kan zargin da ya yiwa Buhari

- Wata kungiya ta yi watsi da harin da babban lauyan da ke kare hakkin dan adam, Femi Falana ya kai kan shugaba Buhari

- Kungiyar ta ce ikirarin da Falana ya yi na cewa shugaba Buhari na renon zarcewa a karo na uku cikin sirri abun dariya ne

- Kungiyar ta NDF ta ce duk wani dan Najeriya da ke bibiyar tsarin shugabancin shugaba Buhari zai san cewa babu wani abu makamancin wanda ake alakantawa da Shugaban kasar

Wata kungiyar damokradiyya, a ranar Lahadi, 10 ga watan Nuwamba, ta caccaki lauyan da ke kare hankin dan adam kuma babban lauyan Najeriya, Femi Falana, akan harin da ya kai wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kwanan nan.

Kungiyar ta National Democratic Front (NDF) ta ce furucin Falana na cewa shugaba Buhari na neman zarcewa a karo na uku a 2023, bai da tushe, ma’ana sannan kuma cewa ko kadan baya bisa hankali.

Babban sakataren kungiyar ta NDF, Abdulkadi Bolaji, ya bayyana babban lauyan a matsayin mai neman suna duk da cewar Buhari ya sha fada lokuta da dama cewa bai da niyan tsawaita wa’adin mulkinsa.

Bolaji ya ce Falana ne kawai ya shirya wannan batu mara tushe na cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na kulla-kullan zarcewa a karo na uku a 2023 cikin sirri.

Ya ce babban lauyan ya yanke shawarar zubar da kimarsa, duk da cewar shugaba Buhari ya sha bayyana kudirinsa na rashin son kara wa’adinsa.

KU KARANTA KUMA: Ina aiki ba ji ba gani don ganin Yahaya Bello ya zarce – El-Rufai

Ya bayyana cewa duk wani dan Najeriya da ke bibiyar tsarin shugabanci irin na shugaban kasa Buhari toh zai san cewa lallai babu wani abu makamancin wanda ake alakantawa da Shugaban kasar cikin lamarinsa.

Ya bayyana cewa wannan furuci na Falana ya kasance abun dariya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel