Motar Soji ta hallaka mutane 2 cikin Keke Napep, 3 sun jikkata

Motar Soji ta hallaka mutane 2 cikin Keke Napep, 3 sun jikkata

Wata babbar motar hukumar Soji ta nike wata keken a daidaita sahu a jihar Yobe inda wata dalibar kwalejin fasahar tarayya dake Damaturu, Hussaina Bello, da wani dan yaro suka rasa rayukansu.

A cewar idanuwan shaida, hadarin ya faru ne sakamakon sabawa dokar hanya daga dukkan bangarorin biyu.

Sauran mutane uku da ke cikin Keken sun jikkata kuma an garzaya da su asibiti.

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bukaci a kaddamar da bincike cikin lamarin a wani jawabi da hadiminsa ya saki.

Jawabin yace: "Mai girma gwamna Mai Mala Buni ya samu labarin hadarin da ya faru a Damaturu jiya inda motar soji ta nike Keke Napep mai dauke da fasinjoji kuma mutane biyu sun rasa rayukansu."

"Gwamna Buni ya umurci sakataren gwamnatin jihar ya hada kai da hukumar soji domin gudanar da cikakken bincike cikin lamarin domin sanin gaskiyar abinda ya faru."

Motar Soji ta hallaka mutane 2 cikin Keke Napep, 3 sun jikkata

Motar Soji ta hallaka mutane 2 cikin Keke Napep, 3 sun jikkata
Source: Twitter

Ya ce kwamandan Task Force Brigade da kwamandan 233 Tank Battalion da wasu jami'an gwamnati sun kai gaisuwar ta'aziyya gidajen yan'uwan wadanda suka rasa rayukansu.

Gwamna Buni ya umurci ma'aikatar ilmin jihar ta tabbatar da an kula da wadanda suka jikkata kuma kyauta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel