Ina aiki ba ji ba gani don ganin Yahaya Bello ya zarce – El-Rufai

Ina aiki ba ji ba gani don ganin Yahaya Bello ya zarce – El-Rufai

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya bayyana cewa yana nan akan jajircewarsa na ganin nasarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamnan Kogi.

Ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 10 ga watan Nuwamba yayinda yake karyata rahoton cewa yana sukar jam’iyyar mai mulki.

A wani jawabi daga Muyiwa Adekeye, kakakinsa, El-Rufai, wanda ya kasance shugaban kungiyar kamfen din APC a zaben, ya ce yana aiki ba dare ba rana domin tabbatar da nasarar Yahaya Bello a karo na biyu.

“Mutanen jihar Kogi Za su zabi wanda suke so a zaben. Don haka, duk wani dan siyasa na da aiki don tabbatar da cewar masu zaben sun yi aiki da bayanai da suka dace, ba wai karya da labarai na bogi ba,” in ji jawabin.

Adekeye ya kara da cewa kowa ya san cewa El-Rufai na bayar da gudunmawarsa a duk ayyukan da aka basa, sannan kuma cewa “babu abunda zai sha banban a zaben Kogi.”

Ya Kara da cewa gwamnan zai bi sahun sauran mambobin kungiyar kamfen din wajen ziyartar Kogi a wannan makon “yayinda APC ke aiki don sake samun zabe bisa damokradiyya.

KU KARANTA KUMA: ‘Dan Majalisa Atigwe ya ba Buhari shawara ka da a bude iyakokin Najeriya

“APC za ta cigaba da kamfen domin samun goyon bayan mutanen Kogi wajen ganin sun sabonta kuri’un da suka ka baiwa jam’iyyarmu na wasu shekaru hudu masu zuwa,” in ji shi.

“Wannan shine muradin Malam Nasir El-Rufai da mambobin kungiyar kamfen din APC.”

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa PDP mai hamayya a Najeriya, ta ce akwai wani shiri a kasa da jam’iyyar APC da kuma gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje su ke yi na canza Alkalan shari’ar karar zaben 2019.

Jam’iyyar adawar ta zargi APC mai mulki da gwamnatin Kano da yunkurin sauya Alkalan da za su saurari karar zaben gwamnan jihar da aka daukaka a gaban kotun daukaka kara da ke Garin Kaduna.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel