‘Dan Majalisa Atigwe ya ba Buhari shawara ka da a bude iyakokin Najeriya

‘Dan Majalisa Atigwe ya ba Buhari shawara ka da a bude iyakokin Najeriya

‘Dan majalisar wakilan tarayya, Honarabul Simon Atigwe, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta cigaba da rufe kan iyakokin kasar na fiye da tsawon shekaru biyu domin jama’a su amfana.

Simon Atigwe mai wakiltar Mazabar Igbo Eze da Udenun jihar Enugu a majalisar tarraya ya yi wannan kira ne a lokacin da ya yi hira da Manema labarai a Ranar Lahadi, 10 ga Watan Nuwamba.

Da ya ke zantawa da ‘Yan jaridar a Garin Abuja jiya sai ya ke cewa: “A na wa ra’ayin wannan shi ne matakin da ya fi kowane kyau da shugaban kasar ya dauka idan ha rana maganar tattalin arziki.”

“Saboda ba za ka bari a maida kasar ka bolar zuba duk wasu kaya daga kasashen waje ba, wannan ya ke sa mutanenka su zama kasalallu; su zama masu karbar kaya maimakon su hada na su.”

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya taya Mamman Daura murnar cika shekaru 80

“Ina ga babu wanda za a taimaka idan aka ce a bude iyakoki domin a shigo da kaya yayin da ake fasa-kaurin da aka gaza shawo kansa. Mu na asarar kudin shiga domin ba a ba mu ko sisi ta fasa-kauri”

“Idan za a rika shigo da kaya ta tashoshin ruwa da na sama, za a rika sa ido a kan abubuwan da ake kawo mana. Bayan kudin shiga kuma, an samu tsaro, domin ana shigowa da makamai a boye.”

“Kasar Sin sun zama abin da su ka zama ne bayan sun garkame kusan duka iyakokinsu na tsawon shekaru 50 ko makamancin haka.” ‘Dan majalisar kasar ya nuna cewa ya na goyon bayan wannan.

A na sa ra’ayin, Atigwe, ya na ganin cewa Najeriya ta na rasa kudin shiga a dalilin fasa-kaurin da ake yi, sannan kuma a kan shigowa Miyagun mutane da makamai idan aka bar iyakokin kasar a bude.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel