Wani fasinja ya yanke jiki ya fadi matacce a filin jirgin saman Malam Aminu Kano

Wani fasinja ya yanke jiki ya fadi matacce a filin jirgin saman Malam Aminu Kano

Wani mutum mai tsakaicin shekaru da aka biye sunansa ya fadi matacce a filin jirgin saman Malam Aminu Kano (MAKIYA) da ke birnin Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa fasinjan, da ke kan hanyarsa ta zuwa Abuja, ya fadi ne a daidai lokacin da yake kokarin shiga cikin jirgin sama.

Wata majiya ta bayyana cewa fasinjan yana tare da wani abokinsa daga jihar Jigawa, wanda zasu halarci wani taro a Abuja.

Ma'aikata a filin jirgin sun garzaya da fasinjan zuwa asibiti bayan faduwarsa, kuma likitoci sun tabbatar da cewa ya mutu.

Kakakin MAKIA, Memuna Tadafe, bata amsa kiran wayar da wasu kafafen yada labarai suka yi mata ba domin jin ta bakinta a kan mutuwar fasinjan.

A wani labarin na Legit.ng, an bayyana cewa iyalan AbdulRasheed Maina sun musanta ikirarin wata kafar yada labarai ta yanar gizo, cewa yana nan a gidan gyaran hali inda yake ikirarin bashi da lafiya kuma yana samun kulawar ma'aikatan lafiya.

DUBA WANNAN: Daukaka guda da marigayi Murtala ne kawai ya samu a cikin tsoffin shugabannin Najeriya a mulkin soji

Iyalan sun bayyana cewa, Maina bashi da cikakkiyar lafiya tun shekaru 15 da suka gabata.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa, ana zargin tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, AbdulRasheed Maina da laifin damfarar kudi har naira biliyan 2.

Ya bayyana a gaban kotun ne kan kujerar guragu don nuna bashi da lafiya kuma ana ta karramashi a gidan gyaran hali da ke Kuje.

Amma kuma iyalansa sun yi saurin maida martani inda suka ce yana da wata cuta da ya dade yana fama da ita kuma Faisal yana da wata cuta ta gado inda yake cikin mummunan hali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel