Yan jam'iyyar APC 21,000 sun koma PDP a jihar Zamfara

Yan jam'iyyar APC 21,000 sun koma PDP a jihar Zamfara

Kimanin yan jam'iyyar All Progressives Congress, APC, 21,000 sun sauya sheka zuwa babbar jam'iyyar da ke ci a jihar Zamfara, Peoples Democratic Party, PDP.

Wadannan suka sauya shekan sun samu tarba daga gwamnan jihar, Bello Matawalle, da shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Alhaji Ibrahim Mallaha, a Gusau, babbar birnin jihar ranar Lahadi.

Yawancin wadanda suka sauya shekarn ya karamar hukumar Maradun ne, mahaifar gwamnan.

A taron, gwamnan ya yabawa sabbin yan PDP kan daukan wannan mataki da zai ciyar da jihar gaba.

Ya yi kira ga mazauna jihar Zamfara su kasance masu bin doka kuma su guji rikice-rikice da zai iya mayar da jihar ruwa.

A jawabin shugaban PDP na jihar, ya yi alkawarin cewa za'a kula da wadannan sabbin yan jam'iyyar kamar yadda ake kula da dukkan sauran 'yayan jam'iyya.

A watan Mayu, kotun koli ta yi watsi da nasarar da yan takaran jam'iyyar APC a jihar a zaben 2019 sakamakon rashin gudanar da zaben fidda gwani.

Kotun sauraron kararrakin zaben kujerar gwamnan jihar Zamfara dake zama a Abuja, tayi watsi da karar da ke bukatar sauke Gwamna Bello Matawalle daga kujerarsa a ranar Litinin.

Karar da Muhammed Takori na jam'iyyar APDA ya shigar akan Matwalle da hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC an yi watsi da ita ne a yau.

Takori da jam'iyyar APDA sun shigar da karar ne da bukatar a sauke Matwalle daga kujerar gwamnan jihar saboda bai ci kuri'u biyu bisa uku na jimillar kuri'un jihar kamar yadda doka ta tanadar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel