Zuwa kotu a keken guragu: Iyalin Maina sun fadi gaskiyar halin da lafiyarsa ke ciki

Zuwa kotu a keken guragu: Iyalin Maina sun fadi gaskiyar halin da lafiyarsa ke ciki

Iyalan AbdulRasheed Maina sun musanta ikirarin wata kafar yada labarai ta yanar gizo, cewa yana nan a gidan gyaran hali inda yake ikirarin bashi da lafiya kuma yana samun kulawar ma'aikatan lafiya.

Iyalan sun bayyana cewa, Maina bashi da cikakkiyar lafiya tun shekaru 15 da suka gabata.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa, ana zargin tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, AbdulRasheed Maina da laifin damfarar kudi har naira biliyan 2. Ya bayyana a gaban kotun ne kan kujerar guragu don nuna bashi da lafiya kuma ana ta karramashi a gidan gyaran hali da ke Kuje.

Amma kuma iyalansa sun yi saurin maida martani inda suka ce yana da wata cuta da ya dade yana fama da ita kuma Faisal yana da wata cuta ta gado inda yake cikin mummunan hali.

DUBA WANNAN: Mayakan Boko Haram 16 tare da matansu sun mika wuya ga rundunar soji

A wata takarda da Abdullahi Usman yasa hannu a madadin iyalin yace, "Hankalinmu ya kai ga wallafar jaridar Sahara Reporters da take nuna karya a ciwon tsohon shugaban fansho na kasa, AbdulRasheed Maina. Ba gaskiya bane da aka ce ana karramasa a gidan gyaran halin. Ana dubasa ne kamar yadda ake wa duk wani wanda aka tsare,"

"Akwai karya da aka ce maina na karbar baki a duk lokacin da yaso. A takaice dai, ganinsa na da wuya fiye da ganin kowa a gidan gyaran halin. Iyalai da abokan arziki da yawa sunyi kokarin ganinsa amma babu dama,"

Maina ya kasance da rashin lafiyar da yake kan magani tun shekaru 15 da suka gabata. Zaku iya tabbatar da hakan daga tarihin lafiyarsa. Maina ya kasance yana shan magunguna kuma lafiyarsa kara tabarbarewa take yi sakamakon rashin magungunansa a gidan gyaran halin. Akwai wani ciwon gado da dansa Faisal ke fama dashi . yana fama da mummunan ciwon baya saboda yanayin wajen da yake tsare."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel