Dankari: DSS ta damke masu satar kananan yara 5 a jihar Kebbi

Dankari: DSS ta damke masu satar kananan yara 5 a jihar Kebbi

Hukumar binciken leken asiri DSS ta damke wasu masu satan kananan yara biyar kan laifin satan yara biyu a karamar hukumar Zuru ta jihar Kebbi.

A cewar DSS, daga cikin wadannan mutanen akwai wata babbar malamar asibiti a asibitin Usmanu Danfodio dake jihar Sokoto.

Malamar asibitin mai suna, Helen Samuel, da abokan aikinta hudu Dorathy Okonkwo, Comfort Nwanko, da Uchenna Benedict yan jihar Anambara da Delta; sannan wani Moses dan garin Zuru a jihar Kebbi.

Wannan ya biyo bayan rahoton da aka samu daga iyayensu, Yusuf Henso da matarsa Rabi Kabiru da suka kai kara ofishin yan sanda kan bacewar yaronta, Hussaini dan shekara 1 da wata 4.

An sace yaron ne yayinda yake wasa kimanin watanni hudu da suka gabata.

KU KARANTA: An damke barauniyar jaririya a filin jirgin saman Aminu Kano

Yan bangan unguwan suka kai karan lamarin ofishin DSS inda aka kaddamar da bincike wanda ya kai ga damke wannan mutane.

Dayan yaron da aka samesu sun sace shine James, kuma sun canza masa suna zuwa Chikasom.

Yayin mayar da yaran wajen iyayensu a gidan gwamnatin jihar dake Birnin Kebbi, gwamnan jihar, Abubakar Bagudu, ya yabawa jami'an tsaron da suka damke wadannan mugun irin.

Ya taya iyayen yaran murnan dawowar yaransu kuma ya yi kiraga da yan jarida su yada irin wadannan mugayen mutane.

Yace: "Gwamnatina za ta cigaba da bada goyon baya ga dukkan jami'an tsaro a jihar domin gudanar da ayyukansu cikin sauki."

A wani labarin kuma, Jami'an Tsaron filin jirgin sama AVSEC na filin jirgin Malam Aminu Kano dake unguwar Takia jihar Kano sun samu nasarar damke wata mata ta saci jaririyar wata shida tana kokarin guduwa da ita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel