Osinbajo: Dattawan Yarbawa ba za su bari a taba VP a Najeriya ba

Osinbajo: Dattawan Yarbawa ba za su bari a taba VP a Najeriya ba

Alamu sun nuna cewa fatattakar wasu Hadimin mataimakin shugaban kasa da aka yi ya dauki wani sabon salo inda Dattawan Yarbawa su ka fito su na kokawa game da abubuwan da ke faruwa.

Kamar yadda rahotanni su ka zo mana daga Jaridar Vanguard, manyan kasar Yarbawan sun bayyana cewa ba za su bari wani mugun abu ya faru da Mai girma Farfesa Yemi Osinbajo ba.

Wannan na zuwa ne bayan an tsige wasu Hadiman da ke aiki a karkashin mataimakin shugaban kasar kwanan nan. Kafin nan kuma an ruguza wani kwamiti da Yemi Osinbajo ya ke jagoranta.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya maye gurbin majalisar EMT na tattalin arziki da EAC wanda za su rika ba shi shawara kai tsaye. Wannan ya sa Yarbawan su ka fara nuna ‘dan yatsa.

Majiyar ta ce Dattawan sun yi gargadi a kan abin da su ka kira tozarta mataimakin shugaban kasa, inda su ka ce ba za su zura idanu wasu gungu su na wulakanta mutum na biyu a kasar ba.

KU KARANTA: Tarihin wasu Mukarraban Osinbajo da Shugaba Buhari ya kora

Wadannan manyan sun bayyana cewa duk wani mummunan abin da ya faru da tafiyar Osinbajo, fito-na-fito ne kan kabilar Yarbawa ba tare da la’akari da banbancin jam’iyyar siyasa ba.

Farfesa Banji Akintoye ya yi magana, ya na cewa: “Na biyu a Najeriya shi ya ke jagorantar majalisar tattalin arziki tun 1999 kuma Osinbajo ya ke rike da wannan matsayi har kwanan nan.”

Akintoye ya ke cewa ba za su kyale wulakancin da ake yi wa ‘Ya ‘yan Yarbawa ba. Farfesan ya kara da cewa wadanda ba su cikin kabilar Fulani kadai ake yi wa wannan wulakanci a gwamnati.

A na sa bangaren, Jagoran kungiyar Afenifere, Pa Ayo Adebanjo, ya ce babu abin da kasar Yarbawa ta amfani da shi a mulkin jam’iyyar APC inda ya daura laifin duk a kan Yemi Osinbajo.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel