SERAP: Kudin tsaro sun sa an shigar da Buhari, Majalisa, dsr, kara a gaban kotu

SERAP: Kudin tsaro sun sa an shigar da Buhari, Majalisa, dsr, kara a gaban kotu

Mun ji cewa kungiyar nan ta SERAP mai bin diddikin ayyukan zamantakewa da tattalin arziki a Najeriya ta shigar da shari’a a gaban babban kotun tarayya da ke Garin Abuja a kan kudin tsaro.

SERAP ta bukaci kotu ta tursasawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan su yi bayani game da yadda su ka kashe kudin da ake warewa da sunan tsaro.

Wannan kungiya ta hada har da shugaban majalisa wakilai, Femi Gbajabiamila, wajen fitowa ayi wa mutanen Najeriya bayanin inda su ka raba kudin tsaro da kuma yadda aka kashe su tun daga 1999.

Kamar yadda mu ka ji daga bakin kungiyar da kan ta, ta na so a sa manyan kasar su wallafa bayani dalla-dalla game da yadda gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi su ka kashe kudin.

SERAP ta na so jama’a su samu bayani kan inda kudin tsaron kasar su ka shiga daga 1999 zuwa bana. An shigar da wannan kara ne a takarda mai lamba FHC/ABJ/CS/1369/2019 a Ranar 8 ga Nuwamba.

KU KARANTA: Ana zargin Gwamnan APC da shirin cafke Dino Melaye daf da zaben Kogi

Kungiyar ta dogara ne da dokar FOI wanda ta ba ‘yan kasa damar samun duk wasu bayanai daga bakin gwamnati wajen fayyace mata inda ta kai Naira biliyan 241.1 da aka kasafta domin inganta tsaro.

Ana raba wannan makudan kudi ne a fadin jihohi da kananan hukumomi 744. Daga cikin wadanda ake so su bada bayani a kotu har da gwamnan babban bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele.

SERAP ta ambaci sunan babban Akawu da mai binciken kudi a Najeriya, Ahmed Idris da Anthony Ayine a wannan shari’a. Kungiyar ta ce a dokar kasa, ta na da hakkin jin inda kudin mutane ya ke tafiya.

Lauyoyin kungiyar; Kolawole Oluwadare da Opeyemi Owolabi, sun fadawa kotu a takarda cewa idan ba a bin diddiki, babu yadda za a iya maganin rashin gaskiya wajen kason kudin tsaro a Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel