2019: Yadda PDP da APC za su kaya da juna a zabukan Kogi da Bayelsa

2019: Yadda PDP da APC za su kaya da juna a zabukan Kogi da Bayelsa

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ‘yan takara 69 ne za su kara domin neman kujerar gwamna a zaben jihohin Kogi da Bayelsa. A Ranar 16 ga Watan Nuwamba za a fara wannan gwabzawa.

Jam’iyyun APC da PDP su ne su ka fi karfi a zabukan da za a yi inda kowanensu ya ke kokarin samun nasara. PDP ce mai rike da mulki a Bayelsa, yayin da jihar Kogi ta ke hannun APC a yanzu.

A jihar Bayelsa, jam’iyyu 45 ne su ka fito takarar sabon gwamnan da za ayi. Douye Diri na jam’iyyar PDP ya yi Kwamishina a jihar, kuma tsohon ‘Dan Majalisa ne sannan Sanata ne mai-ci.

A bangare guda kuma David Lyon wanda APC ta tsaida domin tunbuke PDP a jihar Bayelsa ya na da karbuwa wurin jama’a saboda kyauta da taimakonsa wajen samawa mutanen jihar aikin yi.

Jaridar Daily Trust ta ce Diri ya na da matukar karbuwa a shiyyoyin Sagbama, Kolokuma/Opokuma. Abokin takararsa kuma ya na da jama’a a Yenagoa da cikin Garin Ekeremor.

KU KARANTA: Ban yi makaranta ba a lokacin da na auri Mijina - Uwargidar Jihar Bauchi

A jihar Kogi, akwai ‘yan takara 22 da ke shirin goge-raini da gwamna mai-ci na APC watau Yahaya Bello. Daga ciki har da Natasha Akpoti ta jam’iyyar SDP da aka nemi a hana takara a da.

Yahaya Bello zai fafata a jihar Kogi ta tsakiya inda ke da kuri’a fiye da 400, 000 bayan ya dauko mataimakinsa daga yankin Gabashin Kogi wanda a nan mutanen Kabilar Igala su ka fi yawa.

Wada Musa na PDP ya na cikin Kabilar Igala wadanda su ka dade su na mulkin jihar kuma su ka rasa mulki bayan rasuwar Abubakar Audu. A nan ne kusan 50% na kuri’un jihar Kogi za su fito.

A Yammacin jihar Kogi kuma inda Smart Adeyami da Sanata Dino Melaye su ka fito, APC ta yi kokarin jawo manyan ‘yan siyasa domin toshe karfin ‘dan takarar mataimakin gwamnan PDP.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel