Data: Gwamnatin Najeriya ta shirya rage farashi da maganin coge

Data: Gwamnatin Najeriya ta shirya rage farashi da maganin coge

Hukumar NCC mai kula da kamfanonin sadarwa ta ce ta na aiki domin dabbaka umarnin da gwamnatin tarayya ta bada na duba koke-koken zaftarewa jama’a ‘data’ da ake yi a kasar nan.

Haka zalika a wata takarda ta hukumar ta aikawa Mai girma Minista, Dr. Isa Ali Pantami, ta ce ta na kan duba lamarin rage farashin ‘data’ da ake amfani da shi wajen hawa shafukan yanar gizo.

Mai magana da yawun Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Misis Uwa Suleiman, ta bayyana wannan a wani jawabi da ta fitar daga babban birnin tarayya Abuja a jiya Ranar Asabar.

Kakakin Ministar ta ce: “Wannan martani ne game da wa’adin kwanaki biyar da Minista ya ba hukumar domin kawo karshen matsalar zaftarewa mutane ‘data’ da ake yi ba tare da ka’ida ba.”

“NCC sun yi bayani a wasikarsu cewa sun sanar da dukannin kamfanonin sadarwa game da hukuncin sabunta ‘data’ da ake yi da karfi da yaji tare da tilastawa mutane sayen wasu hajojin.

KU KARANTA: Pantami ya takawa MTN burki bayan sun kawo wani sabon tsarin USSD

“Sun lissafo ukubar da aka gindaya wanda su ka hada da tarar kudi ga kamfanonin da su ka saba doka.” Suleiman ta ce bayan umarnin Ministar, hukumar ta duba dokar NCC ta shekarar 2003.”

Yanzu haka dai hukumar ta NCC ta na sake ziyarar dokar da ta kafa ta a 2003 tare da irin ikon da ta ke da shi da karfin da doka ta ba ta. Jawabin ya ce watakila nan gaba a fitar da wani bayanin.

Har ila yau, NCC ta sanar da Pantami game da ka’idar ta da bada na dawowa wanda aka zare kudinsa domin samunta masa sayen ‘data’ ba tare da ya bukata daga kamfanonin sadarwar ba.”

Hukumar ta sanar da Ministan irin kokarin da ta ke yi dare da rana domin cika umarnin da ya bada. Ta kuma bukaci karin lokacin wa’adin da aka bada na 8 ga Nuwamba domin daukar mataki.

Mai magana da yawan Ministar ta ce Isa Ali Pantami ya amince da wannan roko da hukumar ta yi inda ya kara da cewa gwamnatin tarayya ba za ta bari a rika cutar mutanenta babu wani dalili ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel