Kano: A cafke Iyayen da aka sace ‘Ya ‘yansu saboda sakacinsu – Sanusi

Kano: A cafke Iyayen da aka sace ‘Ya ‘yansu saboda sakacinsu – Sanusi

Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi ya tofa albarkacin bakinsa a game da wasu kananan yara da aka sace daga jihar Kano inda aka tsere da su zuwa Garin Onitsha da ke jihar Anambra.

Daily Nigerian ta rahoto Sarkin ya na cewa ya kamata a daure Iyayen da su ka yi sake har aka sace ‘Ya ‘yansu. Muhammadu Sanusi II ya ce Iyayen sun kyale yaran ne su na gararamba.

Sarkin na Birnin Kano ya yi wannan jawabi ne wajen wani taro da wata kungiya mai suna LESPADA ta shirya domin wayar da kan jama’a a kan illar shaye-shaye a Ranar 9 ga Nuwamba.

“A game da batun satar yaran Kano, ina magana da Sarkin Onitsha a kan batun. Mu na bin kadin lamarin.” Inji Sarkin na Birnin na Kano.

“Mun ji maganganu iri-iri ana sukar Inyamurai cewa an sace Yaranmu. Inyamurai masu satar mutanen sun shiga har gida ne sun sace yaran? Ko kuwa kun kyale ‘ya ‘yanku ne su na tangadi a gari.”

“Dole mu fadawa kanmu gaskiya. Lokacin da Iyayen farko na yaran su ka kawo kara wuri na, na ce, da ina da iko, da na jefa Iyayen a gidan yari.”

KU KARANTA: Majalisa ta fadawa Buhari hanyoyin rage garkuwa da Bayin Allah

“Sai da na bada umarni a tambayi Kwamishinan ‘yan sanda ko akwai dokar maganin sakaci. Na tambaya ba mu da wannan doka? Duk wanda ya kawo kukan an sace masa yaro ‘dan shekara hudu a wajen wasa ya kamata a daure shi, laifin sakaci ne!”

“Dole Bahaushe ya canza tunaninsa. Sai mu yi ta daura zargi a kan Ibo da Yarbawa, bayan laifin mu ne."

Sarkin ya kara da: “Ka yi kokarin sace yara a Onitsha ka gani ko za ka iya samun wanda za ga dauke. Ko ba haka ba ne? Su na barin yaransu' yan shekaru uku ko hudu su na yawon bara a titi?

Sarkin na Kano ya nuna cewa ba za a ce sauran mutanen ba su da laifi ba amma ya ce tun farko Malam Bahaushe ya yi sake da ya ke tura yara su yi bara saboda iyayensu ba su da wadata.

Mai martaban ya yi magana a game da yaran da su ke nutsewa a cikin rijiya inda ya ce iyayensu ne su ka kashe su da sakacinsu ba kowa ba. Sanusi II ya koka da rashin soyayya a gidajen aure.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel