Ina yar shekara 16 na auri mijina, ko firamari ban yi ba - Uwargidar gwamnan Bauchi

Ina yar shekara 16 na auri mijina, ko firamari ban yi ba - Uwargidar gwamnan Bauchi

Aishatu Mohammed, Uwargidar gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ta bayyana a ranar Asabar cewa bata yi karatu ba lokacin da ta auri mijinta.

Haijya Aishatu ta bayyana hakan ne a jihar Bauchi a taron da kwamitin tallafin kananan yaran ta majalisar dinkin dunya UNICEF.

Tace: "Ina yar shekara 16 kuma a jahilce lokacin da na auri mijina."

"Mu yara mata 100 ne a danginmu; babu wacce tayi karatun Boko cikinmu; sai da na haifi yara uku na fara karatu."

"Dalilin haka shine iyayenmu basu yarda da ilmantar da diya mace ba; na yi kokarin zuwa makaranta amma basu yarda ba."

"Na kudirci zuwa makaranta daga yayyuna bayan haihuwana na uku, na nace sai da mijina ya samar mun malami a gida."

"Da haka na fara sannan na tafi makarantar sakandare. Yau na kammala karatun Digiri a jami'ar Abuja."

DUBA WANNAN:An damke tsohon Soja mai sayarwa yan siyasa jarirai

Ta bayyana yadda rashin ilmantar da yara mata da aurar da su da wuri yayi tsamari a jihar inda ta daura laifin kan iyaye da sukayi imanin cewa diya mace ba ta bukatar zuwa makaranta.

Hajiya Aisha ta jaddada muhimmancin ilmantar diya mace da kananan yara ga baki daya saboda hakan zai rage yawan laifuka rashin tarbiyya cikin al'umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel