Yawan matasan da suka samu N-Power: Daga Kano sai Kaduna - Hadimin shugaban kasa

Yawan matasan da suka samu N-Power: Daga Kano sai Kaduna - Hadimin shugaban kasa

Hadimin shugaba Muhammadu Buhari kan shirye-shiryen jin dadin al'umma, Isma'eel Ahmad, ya bayyana jihohin da fi samun aikin wucin gadi ta N-Power.

A wata hira ta musamman da Legit.ng tayi da shi a makon nan, Barista Isma'eel ya bayyana cewa yan Arewa sun samu kashi 55 zuwa 60 a matasa 500,000 da aka dauka a shirin.

Hakazalika ya bayyana cewa kimanin kashi sittin na matasan sun fara dogaro da kai ta N30,000 da ilimin da suke samu a shirin musamman yanzu da ake shirin yaye wadanda aka dauka a shekarar 2016.

A jawabinsa, daga jihar Kano sai Kaduna sai Benue a yawan matasan N-Power.

Yace: "Jihar da tafi kowani mutane yawan yan N-Power jihar Kano ce, jiha ta biyu da tafi yawan mutanen N-Power Kaduna ce, jiha ta uku da tafi Benuwe ce."

"Kaga duk jihohin nan guda uku jihohin Arewa ne. Arewa saboda ta fi yawan jihohi da jihohi 19...kashi 55 zuwa 60% ne yan Arewa."

Da wakilinmu ya tambayeshi kan yawan yan jihar Kano kuwa ya bayyana cewa : "Mutum 18,001 ne yan jihar Kano."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel