Yanzu-yanzu: APC ta samu gagarumin nasara, Akpabio ya samu nasara a kotu

Yanzu-yanzu: APC ta samu gagarumin nasara, Akpabio ya samu nasara a kotu

Kotun daukaka kara dake zamanta a garin Kalaba, babbar birnin jihar Kross RIba, ta yanke hukunci kan zaben kujerar Sanatan mazabar Ikot Epkene a jihar Akwa Ibom.

Kotun ta kwace kujeran Sanatan PDP, Dakta Chris Ekpenyong, wanda aka alanta matsayin zakaran zaben 23 ga Febrairu, 2019 da ya kayar da ministan Neja Delta, Godswill Akpabio.

Da farko kotun zaben dake Uyo karkashin Alkali Akanbi, ta tabbatar da nasarar PDP amma Akpabio ya kai kara kotun daukaka kara dake Kalaba.

Kotun ta baiwa hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta umurnin gudanar da sabuwar zabe cikin kwanaki 90.

KARANTA: Gwamnan Borno ya tallafawa yan kasuwar da shagunansu suka kone da N60m

A ranar Alhamis, Kotun daukaka kara da ke Owerri a ranar Alhamis ta jaddada nasarar Sanata Rochas Okorocha, a zaben sanata mai wakiltar mazabar Imo ta yamma da ta gabata.

Shugaban kungiyar alkalan, R. A Ada, wanda ya karanto hukuncin, yace daukaka karar da Osita Izunaso na jam'iyyar APGA da Jones Onyereri na jam'iyyar PDP suka yi ta kalubalantar nasarar Sanata Okorocha bata da makama.

Hakazalika a ranar, Bulaliyar majalisa, Orji Uzor Kalu, ya samu nasara a kotun daukaka kara inda ta tabbatar da shi matsayin sahihin wanda ya lashe zaben kujeran Sanata mai wakiltar jihar Abiya ta Arewa.

Orji Kalu ya bayyana godiyarsa ga Allah kan wannan nasara da ya samu a kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel