Kotun daukaka kara ta tabbatarwa Gwamna Sanwo-Olu nasararsa

Kotun daukaka kara ta tabbatarwa Gwamna Sanwo-Olu nasararsa

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Legas a ranar Asabar ta tabbatar da nasarar Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta ruwaito cewa alkalai biyar na kotun cikin hukunci biyu da suka yanke sun jadada nasarar Sanwo-Olu a zaben ranar 9 ga watan Maris kana sunyi watsi da daukaka karar da dan takarar gwamna na jam'iyyar Labour Party (LP) da Alliance for Democracy (AD) suka shigar.

Jam'iyyun biyu da 'yan takararsu sun daukaka kara kan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe na jihar Legas ta yi na tabbatar da nasarar Sanwo-Olu kamar yadda INEC ta sanar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Ire-iren abinci 5 da ya kamata dan adam ya guda kafin kwanciya barci

Kotun daukaka karar da tabbatar da hukuncin da kotun sauraron karrakin zabe ta yanke kan cewa wadanda suka shigar da karar sun gaza gabatar da gamsassun hujojji da ke nuna cewa Sanwo-Olu bai cancanta tsayawa zaben na ranar 9 ga watan Maris ba kan ikirarin cewa yana da matsalar kwakwalwa.

Kotun zaben ta ce babu wata kwakwarrar hujja da aka gabatar kan ikirarin da aka yi na cewa Sanwo-Olu na da matsalar kwakwalwa.

Kotun daukaka karar ta jadada hukuncin da kotun zaben ta yanke kan cewa babu hujja kan zargin hadin baki da cin zarafin sojojin Najeriya.

Ta kuma tabbatar da cewa wadanda suka shigar da karar sun gaza nunawa kotu cewa an yi magudin zabe.

Kotun daukaka karar ta umurci wadanda suka shigar da karar su buya kudi N200,000 ga mutane shida da suka yi kararsu (banda kwamishinan 'yan sanda). Jimlan kudi naira miliyan 2.4.

A yayin da ta ke karanto hukuncin a madadin sauran alkalan biyar, Mai shari'a Hannatu Sankey ta ce daukaka karar da aka yi ba ta da madogara haka yasa aka yi fatali da ita.

Ta ce, "Na jadada hukuncin da kotun sauraron karrakin zabe na jihar Legas ta yi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel