Gwamnan Borno ya tallafawa yan kasuwar da shagunansu suka kone da N60m

Gwamnan Borno ya tallafawa yan kasuwar da shagunansu suka kone da N60m

Kamar yadda yayi alkawari tun yana kasar Saduiyya, Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya tallafa yan kasuwar GSM da sukayi asarar dukiyoyinsu sakamakon gobarar da ta ci kasuwa da makudan kudi.

Gwamnan ya taimaka musu da kudi milyan sittin domin rage zafin asarar da sukayi sakamakon gobarar.

An yi asarar shaguna da dukiyoyin miliyoyin naira a gobarar da ta lashe kasuwar waya a daren Alhamis, 31 ga Agusta, 2019 a Maiduguri, birnin jihar Borno.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta bayyana cewa gobarar ta fara ne misalin karfe 8 na dare kuma sai da aka kwashi sa'ao'i kafin yan kwana-kwana, jami'an tsaro da al'ummar gari suka kashe wutar.

Kasuwar da ta shahara da Kasuwar Jagol na dauke da dubunnan kananan yan kasuwa da masu aikin hannu a Maiduguri.

Kakakin hukumar kwana-kwanan Borno, Ambursa Pindar, ya tabbatar da faruwan hadarin kuma yace hukumar za ta gudanar da bincike kan irin asarar da akayi.

Abdulrahman Tahir, wani mai idon shaida ya ce wutan ya fara ne daga wani shago kafin ya kama sauran shagunan kasuwar.

A lokacin, Gwmanan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya umurci shugaban ma'aikatansa, Babagana Wakil, da wasu kwamishanoni biyar su kai ziyara kasuwar kuma su duba irin asarar da akayi domin sanin irin taimakon da gwamnatin za tayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel