PDP ta bukaci Fashola da ya aje aiki akan tsokacinsa kan titunan kasar nan

PDP ta bukaci Fashola da ya aje aiki akan tsokacinsa kan titunan kasar nan

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP tayi kira ga ministan aiyuka da gidaje, Babatunde Fashola, da ya aje aiki sakamakon tsokacinshi akan halin da titunan kasar nan ke ciki.

"Titunan kasar nan ba wasu lalatattu bane kamar yadda ake fadi. Nasan wannan zai zamo kanun labaranku amma titunan ba sa cikin mummunan halin da ake fada," ya sanar da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa a Abuja ranar Laraba.

A maida martanin jam'iyyar PDP wanda mai magana da yawunta yasa hannu, Kola Ologbodinyan, a ranar Juma'a, ta kwatanta kalaman da munanan kalamai, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Jam'iyyar ta bukaci ministan da ya ajiye aiki kuma ya ba 'yan Najeriya hakuri akan wannan maganar tashi.

DUBA WANNAN: Ku amshe kudin PDP amma kada ku zabesu, dan takara a Bayelsa ya shawarci masu zabe

Dan majalisar wakilai kuma dan kwamitin aiyuka a majalisar tarayya, Bamidele Salam, ya kalubalanci ministan da yayi tafiyar titi ta watanni uku a fadin kasar nan don ganin halin da titunan kasar nan ke ciki.

Har yau dai, fashola bai karbi kalubalen ba kuma bai maida martani akan maganar PDP ba.

Hakazalika, jam'iyyar PDP ta bukaci APC da ta bar zancen mulkin PDP na shekaru 16 kuma ta cika alkawarurrukan da tayi wa 'yan Najeriya. Jam'iyyar APc ta saba dora laifi akan jam'iyyar adawar na rashin yin mulkin da ya dace tun daga 1999 zuwa 2015.

Takardar da jam'iyyar ta fitar tace: "Tsokana ne ga sama da mutane miliyan 200 na 'yan Najeriya tare da kuma nuna halin ko in kula da gwamnatin Buhari ke wa 'yan Najeriya wadanda suka rasa rayukansu da wadanda ke rasawa kullum sakamakon tabarbarewar titunan kasar nan".

"Kowanne dan Najeriya yasan cewa manyan titunan da ke fadin kasar nan na mugun hali. Hakazalika, tafiye-tafiye a titunan tashin hankali ne tare da barazana ga rayuwa tun shekaru hudu da suka gabata". In ji takardar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel