Ku amshe kudin PDP amma kada ku zabesu, dan takara a Bayelsa ya shawarci masu zabe

Ku amshe kudin PDP amma kada ku zabesu, dan takara a Bayelsa ya shawarci masu zabe

- Dan takarar jam'iyyar APC a zaben jihar Bayelsa da ke karatowa, David Lyon ya yi kira ga jama'ar jihar da su karbe kudin PDP amma kada su zabesu

- Ya bayyana cewa, jam'iyyar PDP na tattara kudaden da yakamata a habaka jihar dasu don amfaninsu a zaben me zuwa

- Sun san basu cancanci kuri'unka bane shiyasa zasu yi amfani da kudi don siyanku, cewar dan takarar

David Lyon, dan takarar kujerar gwamnan jihar Bayelsa a karkashin jam'iyyar APC a zaben 16 ga watan Nuwamba da ke gabatowa, yayi kira ga jama'ar jihar da su karbe kudi daga PDP a jihar amma su saka wa APC kuri'unsu.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa hukumar kwastam ta hana kai man fetur garuruwa kusa da iyakoki

Yayin jawabi lokacin yakin neman zabensa a garin Okpoama, garin tsohon gwamnan jihar, Chief Timipre Sylva, ya yi bayanin cewa, a maimakon PDP ta habaka jihar, tana nan tana tara kudade don zaben kujerar gwamnan jihar da ke karatowa.

Ya ce: "Ina da tabbacin cewa PDP na ta tarkata kudin da aka ware don habaka al'ummar jihar nan. Amfanin da zasu yi da kudin kuwa shine siyan kuri'unku a ranar zabe saboda sun san basu cancanci kuri'unku ba. Sun san sun ci amanarku. Sakona gareku shi ne ku karbe kudaden amma kada ku zabesu."

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa kungiyar gwamnonin Najeriya za su hada kai don fidda 'yan Najeriya miliyan 24 daga kangin talauci daga yanzu zuwa shekarar 2030.

Mai magana da yawun kungiyar, Abdulrazak Bello-Barkindo ne ya bayyana hakan a babban birnin tarayya Abuja kamar uadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Bello-Barkindo ya ce za su cimma hakan ne cikin wata hadin gwiwa da kungiyar gwamnonin za su yi tare da ofishin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel