2023: Matasan Ohanaeze Ndigbo sunyi muhimmin kira ga Atiku

2023: Matasan Ohanaeze Ndigbo sunyi muhimmin kira ga Atiku

Matasan kungiyar Ohanaeze Ndigbo na duniya sun yi kira ga dan takarar jam'iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar akan kada ya fito takarar shugabancin kasa a 2023 don share fagen bayyanar dan takara daga yankin kudu maso gabas na kasar nan.

Shugaban kungiyar, Okechukwu Isiguzoro, a takardar da ya fitar ranar Juma'a, yayi kira ga Atiku da ya nuna dattako ta hanyar yin burus da kiranshi da ake yi da ya fito takara. Ya kare halin dattakonsa kuma ya mutunta yarjejeniyar da ke tsakanin arewa da kudu.

Isiguzoro yace, yana da tabbacin mulki zai koma kudu a zaben shugabancin kasa na 2023. Yayi kira ga gagaruman jam'iyyun siyasa biyu na PDP da APC da su tabbatar sun bada tikitinsu ga dan yankin kudancin kasar nan a 2023.

DUBA WANNAN: FG tace babu amincewarta wani tsohon gwamna kuma sanata a yanzu ya shigo da makamai

Yace, "Kungiyar matasan Ohanaeze Ndigbo ta duniya na da tabbacin mulki zai koma kudu kuma muna kira ga dan takarar jam'iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar da kada ya takura wajen samun tikitin PDP a 2023. Ya nuna dattako tare da ramawa kabilar Igbo kokarin da suka mishi wajen goyon bayanshi a 2019."

"PDP da APC su mika tikitinsu na shugabancin kasa a 2023 ga kudu a matsayin hanyar nuna mutunta yarjejeniyar mulkin karba-karba. Hakan kuwa shine zai kawo daidaito ta bangaren hadin kai a kasar nan da kuma inganta damokaradiyya tun a 1999," ya kara da cewa.

"Duk wani yunkurin tozarta wannan yarjejeniyar zai habaka wutar rashin yarda ne da kiyayya. Don daidaito da adalci ya tabbata, yankin kudu maso gabas ne yafi cancanta da shugabancin kasa a 2023." ya kammala cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel