APC da PDP sunyi musayar kalamai kan zaben gwamnan jihar Kogi

APC da PDP sunyi musayar kalamai kan zaben gwamnan jihar Kogi

Direktan yakin neman zaben Bello/Onoja, Smart Adeyemi ya yi kira ga Hukumar Yaki da Rashawa ta ICPC ta sanya idanu kan zaben gwamnan jihar Kogi da za a gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamba a jihar.

The Punch ta ruwaito cewa Adeyemi ya yi wannan kirar ne a yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Juma'a a Lokoja inda yace ana bukatar ICPC da EFCC a yayin zaben domin su rika lura da yadda jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ke neman amfani da kudi don siyan kuri'un masu zabe.

Ya ce, "Binciken da jam'iyyar APC ta yi kan dalilan da yasa jam'iyyar ta PDP ba ta yin kamfe ya nuna cewa sun tara mukuden kudade da za suyi amfani da shi wurin bawa INEC da alkalai cin hanci bayan sun sha kaye a zaben.

DUBA WANNAN: Asibitin Malam Aminu Kano yayi aikin kwakwalwa karo na biyu cikin nasara

"Wani dan siyasa daka Kudu maso Yamma ya yi alkawarin bawa jam'iyyar PDP gudunmawar kudu da niyyar kawo rudani a zaben da kuma sayan alkalai. Mu a jam'iyyar APC ba za mu nade hannu muna kallo wasu su kakabawa al'umma gwamna da sanatan da ba su kauna ba."

Sai dai a bangarensa, Mai magana da yawun kungiyar kamfen din Wada/Sam, Faruk Adejoh ya kira zargin da APC ta yi 'abin dariya'.

Adejoh ya ce, "Ai ba mu da kudin kamfen ma balle ayi zancen cewa sun tara wasu mukuden kudi domin wani bukata na daban. Su ne suke da kudade da suke amfani da shi suna daukan nauyin 'yan bangan siyasa.

"Gwamba Bello ya karbi a kalla naira biliyan 540 a cikin shekaru hudu da suka shude ba tare da ya tsinana wasu ayyukan a zo a gani ba. Sun san cewa ranar kin dillanci yana zuwa shi yasa suke ta maganganu duk da cewa sun san ba mu shirya wata manakisa ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel