2030: 'Yan Najeriya miliyan 24 zasu fita daga kangin talauci - FG

2030: 'Yan Najeriya miliyan 24 zasu fita daga kangin talauci - FG

Kungiyar gwamnonin Najeriya sun shirya tsaf don hada kai da gwamnatin tarayya wajen fidda 'yan Najeriya miliyan 24 daga talauci a 2030.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a jawabin da shugaban yada labarai da hulda da jama'a na kungiyar, Abdulrazaque Bello-Barkindo yayi a garin Abuja a ranar Juma'a, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Bello-Barkindo yace, an yi shirin ne na hadin guiwa tsakanin kungiyar gwamnoni da ofishin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.

Yace an tattauna lamarin ne a ranar Litinin a jihar Kaduna da kuma jihar Ekiti a aranar Alhamis.

DUBA WANNAN: Kotu ta kwace kujerar mataimakin kakakin majalisar wata jiha a arewa

Kamar yadda yace, manufar cibiyar habaka dan adam din ta karkata ne a bangarorin ilimi, kiwon lafiya da nagartaccen abinci sai aiyuka.

Ya ce, kungiyar jigon aikin, wacce ta samu shugabanci Yosola Akinbi na ofishin mataimakin shugaban kasar sun fara zagayen wayar da kai a jihar Kaduna.

Yace, Mr Akinbi a jihar ya samu haduwa da Gwamna Nasir El-Rufai da kuma shugaban kungiyar habaka dan adam (HCD) Sagir Ahmad.

Bello-Barkindo yace, duk da habakar aiyukan HCD a jihar Kaduna, ta'ammali da miyagun kwayoyi da matasa ke yi yana zama kawo koma baya a lamarin. Ya kara da cewa, shan miyagun kwayoyin ne tushen duk wasu ta'addanci a jihar.

A bangaren shugaban kungiyar gwamnonin Najeriyar, kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, yayi alkawarin maida hankali wajen cimma manufar HCD.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel