Gungun yan bindiga sun kaddamar da hari a wajen daurin aure, mutum 1 ya mutu

Gungun yan bindiga sun kaddamar da hari a wajen daurin aure, mutum 1 ya mutu

Wasu gungun miyagu yan bindiga sun kaddamar da mummunan hari a wani wajen daurin aure a unguwar Ndiya Ikot Ukah cikin karamar hukumar Nsit Udium na jahar Akwa Ibom, inda suka kashe mutum daya.

Jaridar Punch ta ruwaito yan bindigan sun kashe wannan mutumi mai suna Godwin Thomas a yayin da tsaka da bikin daure a ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba, bikin da hatta gwamnan jahar, Udom Emmanuel ya samu halarta.

KU KARANTA: An zabi Musulmai maza da mata 26 mukaman siyasa a kasar Amurka

Yan bindigan sun dira gidan bikin ne jim kadan bayan gwamnan jahar ya tashi ya tafi, a daidai wannan lokaci ne suka kashe Godwin. Sai dai gwamnan ya bayyana damuwarsa bisa kisan matashin, sa’annan ya umarci jami’an tsaro su tabbata sun gano masu hannu cikin kisan.

Cikin wata sanarwa da kwamishinan watsa labarun jahar, Charles Udoh ya fitar, yace Gwamna Udom Emmanuel ya jajanta ma iyalan mamacin, kuma ya yi alkawarin gwamnatinsa za ta cigaba da kokarin kare rayuka da dukiyoyin jama’an jahar.

“Gwamnan jahar Akwa Ibom ta samu labarin harin da wasu miyagu suka kai a garin Ndiya Ikot Ukab cikin karamar hukumar Nsit Ubium inda suka kashe mutum daya a ranar Alhamis, Gwamna Udom ya yi alhinin wannan abu daya faru a ranar da ake cikin farin ciki.

“Don haka ya yi kira ga hukumomin tsaro da su tabbata sun zakulo duk masu hannu cikin harin, tare da gurfanar dasu gaban kotu domin fuskantar hukuncin daya dace da laifin da suka aikata na mutuwar mutumin da bai ji ba, bai gani ba.” Inji shi.

A wani labarin kuma, wata kotun majistri dake zamanta a jahar Kwara ta bayar da umarnin garkame wani matashi bafulatani, Iliyasu Abubakar a kurkukun gwamnatin tarayya dake garin Ilorin saboda tuhumarsa da ake yi da halaka dan uwansa.

Ana tuhumar Iliyasu da kashe yayansa mai suna Isah ne a cikin wani daji dake rugar Fulani ta Gwanara cikin karamar hukumar Baruten na jahar Kwara bayan ya zargeshi da kwanciya da matarsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel