Babu wanda ya fi karfin shugaban kasa Buhari ya juya shi yadda ya so – Fadar shugaban kasa

Babu wanda ya fi karfin shugaban kasa Buhari ya juya shi yadda ya so – Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na da cikakken iko a kan gwamnatinsa, don haka babu wanda ya fi karfin shugaban kasa ya juya shi, inji kaakakin shugaban kasa, Garba Shehu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Shehu ya bayyana haka ne cikin wasu rubuce rubuce da ya yi a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Twitter @Garshehu, cikin martanin da yake mayarwa dangane da rahotannin da ake yadawa game da sallamar hadiman mataimakin shugaban kasa Osinbajo.

KU KARANTA: An zabi Musulmai maza da mata 26 mukaman siyasa a kasar Amurka

“Shugaban kasa na da cikakken iko a kan gwamnatinsa. Ya kamata kafafen watsa labaru su daina baiwa wasu mutane karfin ikon da basu da shi, babu wani mutumi da shugaban kasa ba zai iya juya shi ba.” Inji shi.

A hannu guda kuma, Garba Shehu ya tabbatar da batun sallamr hadiman ofishin mataimakin shugaban kasa guda 35, inda yace: “Fadar shugaban kasa na tabbatar da cewa akwai kwaskwarima da ake yi a fadar gwamnati, inda aka sallami wasu masu rike da mukaman siyasa.

“Shugaban kasa ne ya bayar da wannan umarni, kuma manufar hakan shine rage yawan ma’aikata a fadar gwamnati, tare da rage kudin da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati, haka zalika hakan shi ne amsan daya dace ga zargin da ake yi na cewa ma’aikatan gwamnatin tarayya sun yi yawa.” Inji shi.

Daga karshe Garba Shehu ya yi kira ga yan Najeriya dasu yi watsi da duk wasu jita jita da suke ji game a fadar gwamnatin tarayya, inda ya tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo suna aiki tare.

“Dangantaka tsakanin shuwagabannin biyu na nan cikin aminci da girmamawa, tare za su kai kasar nan ga gaci.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel