Zaben Kogi: Manyan yan takara 5 da ka iya samun shiga gidan gwamnati

Zaben Kogi: Manyan yan takara 5 da ka iya samun shiga gidan gwamnati

Kasa da makonni biyu kafin gudanar da zaben gwamna a Kogi wanda za a yi a ranar Asabar, 18 ga watan Nuwamba, yan siyasa sun fara baje kolinsu sannan dukkanin jam’iyyu, musamman wadanda ke gaban suna ikirarin samun goyon bayan mutane domin lashe zaben.

A wannan rubutun, Legit.ng ta lura da yadda yan takarar ke murza kambun siyasarsu a tseren yayinda kowa ke kokarin ganin ya yi nasarar samun shiga gidan Lugard na shekaru hudu masu zuwa.

Daga bayanan da aka samu daga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), yan takara 23 ne za su yi takarar kujerar gwamnan Kogi. Amma a bisa ga jam’iyyarsu, tseren zai kasance ne a tsakanin manyan yan takara biyar a jihar.

Daga cikin jam’iyyu 23 da ke takara a zaben, ana ganin jam’iyyu biyar ne suka fi karfi sannan tseren zai kasance a tsakanin yan takararsu ne. Wadannan jam’iyyu sune: All Progressives Congress (APC), Peoples Democratic Party (PDP), Accord Party (AP), Social Democratic Party (SDP) fa kuma All Progressives Grand Alliance (APGA).

1. APC/Yahaya Bello

Jam’iyyar All Progressives Congress ce mai mulki a jihar. Dan takarar jam’iyyar a zaben shine Yahaya Bello, ya kuma kasance gwamna mai ci a jihar sannan ya neman tazarce.

Ana ganin cewa duk da cewar shine mai mulki a yanzu, wanda hakan na nufin yana da karfi sosai, sai dai kuma dan takarar PDP, Musa Wada na iya yi masa bazata.

Bello na da goyon baya daga fadar shugaban kasa, da manyan jiga-jigan jam’iyyar da suka hada da tsohon gwamnan jihar Lagas, Asiwaju Bola Tinubu, shugaban jam’iyyar na kasa da takwarorinsu daga jihohin da ke karkashin kulawar APC.

2. PDP/Musa Wada

PDP ta kuma kasance babbar jam’iyya da ke da karfi sosai da kuma damar cin zaben gwamnan na ranar 16 ga watan Nuwamba. Ta bangaren shaharar dan takarar a jihar, PDP da abunda ake bukata wajen karawa da APC sosai a zaben.

Wada wanda ya fito daga kabilar Igala wacce ta kasance mafi girma a jihar na da damar samun kuri'u mafi yawa.

Bayan kasancewarsa Igala, Wada ya fito daga karamar hukumar Dekina wacce ke da karfin zabe a tsakanin kananan hukumomi 21 da ke jihar.

3. AP

Dan takarar gwamna na jam'iyyar Accord Party (AP) a zaben, Abdullahi Mohammed, ya kasance babban mai daukar nauyin jam'iyyar. Kafin yanzu ya gwada sa'arsa sannan wannan ne yunkurinsa na biuyu a zaben gwamnan Kogi na 2019.

A 2015, ya kai matakin zabeen fidda gwani kafin ya rasa damar.

4. SDP

Yar takarar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), Barr Natasha Akpoti, ta kasance cikin wasu harkoki da suka cancanci yabop a fadin jihar tun ma kafi ta bayyana kudirinta na takarar zaben.

Akpoti, wacce ta kasance lauya, ta kasance ruwa biyu - Mahaifinta ya kasance likita daga Okene a Kogi ta tsakiya, yayinda mahaifiyarta ta fito daga kasar Rasha. Takararta na gwamna ya samu karbuwa a fadin jihar sannan tana iya kasancewa yar takara da za ta bayar da mamaki.

An tattaro cewa Akpoti na da goyon bayan matan Ebira da tarin masoya.

5. APGA

Shielkh Ibrahim, wanda ya kasance tsohon dan APC, shine dan takarar jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a zaben 16 ga watan Nuwamba.

Ya bar jam'iyya akan zargin rashin adalci tsakanin shugabannin jam'iyyar.

Koma dai yaya abun zai kasance a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, za a samu sabon gwamnati a jihar, a nan ne za a san wanda zai yi nasara da wanda zai sha kashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel