Gwamnatin Legas ta rusa ginin Kasuwar da taci gobara ranar Talata (Hotuna)

Gwamnatin Legas ta rusa ginin Kasuwar da taci gobara ranar Talata (Hotuna)

Gwamnatin jihar Legas ta rusa gini mai hawa biya a kasuwar Balogun dake jihar da gobara ta lashe a ranar Talata, 5 ga watan Nuwamba, 2019.

An fara rusa kasuwar ne bayan jami'an kwana-kwana sun kashe wutan ranar Laraba.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ne ya bada umurnin rusa kasuwar yayinda ya kai ziyara wajen.

Hakazalika za'a gudanar da bincike kan gine-ginen da ke kusa da ginin domin sanin idan za'a rusa da su.

Kalli hotunan:

Gwamnatin Legas ta rusa ginin Kasuwar da taci gobara ranar Talata (Hotuna)

Hoto mallakin Channels TV
Source: Facebook

A wani lamarin da ya faru yau Juma'a, wani gini a yankin Ebute Metta da ke birnin Lagas ya kama gobara kimanin sa'o'i 48 bayan wata gobara ta afku a yankin Balogun.

Hotunan afkuwar lamarin ya nuna cewa gobarar ta kama ne ba da wasa ba, domin an gano hayaki na tashi ba da wasa ba.

Zuwa yanzu dai babu wani cikakken jawabi daga mahukunta a jihar akan abunda ya haddasa faruwar gobarar a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel