Kotu ta kwace kujerar mataimakin kakakin majalisar wata jiha a arewa

Kotu ta kwace kujerar mataimakin kakakin majalisar wata jiha a arewa

Kotun daukaka kara da ke zama a Makurdi, babban birni jihar Benuwe ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben majalisar jihar na sauke mataimakin kakakin majalisar jihar, Christopher Adaji.

Kafin a sauke kakakin, dan majalisa ne mai wakiltar mazabar Obimini a karkashin jam'iyyar PDP.

Shugaban alkalan da ya jagoranci alkalai uku sun yanke hukuncin cewa, bayyana Adaji a matsayin wanda ya lashe zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ba tare da anyi zabe a Otega da Ogadagba ba, ya sabawa dokar zabe ta 2010.

Jastis Mbaba ya aminta da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe da ta soke zaben.

"Daukaka karar nan bata da tushe," in ji Jastis Mbaba kuma yayi watsi da karar.

DUBA WANNAN: FG tace babu amincewarta wani tsohon gwamna kuma sanata a yanzu ya shigo da makamai

A don haka ne ya ba hukumar zabe mai zaman kanta umarnin kara yin sabon zabe a akwatuna biyu na yankin cikin kwanaki 90 daga yanke hukuncin kamar yadda kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke.

Jastis Mbaba ya kara da yanke tarar N200,000 ga kowanne daukaka kara da wadanda suka daukaka zasu biya.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, ta bayyana Adaji a matsayin wanda ya lashe zaben da banbancin kuri'u 397 amma kuma kuri'un da aka soke sun kai 1,056 a akwatuna biyu a zaben 9 ga watan Maris, 2019 a mazabar Obimini

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel