Yanzu-yanzu: Babu wanda yafi karfin Buhari ya juya shi - Garba Shehu ya tabbatar da koran hadiman Osinbajo

Yanzu-yanzu: Babu wanda yafi karfin Buhari ya juya shi - Garba Shehu ya tabbatar da koran hadiman Osinbajo

Bayan kwana biyu ana rade-radin cewa shugaba Muhammadu Buhari dake Landan ya sallami wasu hadiman mataimakinsa, Yemi Osinbajo, akalla guda 35 ba tare da wani laifi ba, mai magana da yawun Buhari, Garba Shehu, ya fito ya raba gardama.

Garba Shehu ya bayyana cewa ba wani abu bane don shugaban kasa ya rage hadiman mataimakinsa a duk lokacin da ya ga dama kuma ba shi bane farau ba.

Garba Shehu yace: "Fadar shugaban kasa na son tabbatarwa al'umma cewa akwai sauye-sauye da ake yi cikin gwamnatin nan, musamman rage nade-nade da sallamar wadanda aka nada a wa'adi na biyu."

"Shugaba Buhari ne ya bada umurnin yin hakan domn rage yawan ma'aikata. Hakazalika wannan martani ne ga wadanda suke cewa ma'aikata sun yi yawa a fadar shugaban kasa."

"Ofishin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ta bi umurnin shugaban kasa, kuma ta rage yawan ma'aikatanta."

"Babban dalilin da yasa aka yi haka shine tattalin kudin al'umma da gabatar da ayyukan da jama'a ke bukata."

"Tun da aka fara mulkin nan, yawan hadiman shugaban kasa bai kai na mataimakin shugaban kasa ba kuma an dade ana son rage yawan ma'aikatan fadar shugaban kasa."

"Ba'a rage ma'aikata domin cin mutunci ko rage matsayin ofishin mataimakin shugaban kasa ba, kamar yadda wasu yan fadar shugaban kasa ke nunawa."

"Buhari ke juya mulkinsa. Kafafen yada labarai su daina baiwa wani ikon shugaban kasa. Babu wanda yafi karfin Buhari ya juyashi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel