Wata sabuwa: Yan daba sun shigo Kogi gabannin zaben Gwamna – PDP ta yi zargi

Wata sabuwa: Yan daba sun shigo Kogi gabannin zaben Gwamna – PDP ta yi zargi

- Yan kwanaki kafin zaben gwamnan jihar Kogi wanda za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ja hankalin jami’an tsaro a jihar Kogi zuwa ga zargin cewa yan daba sun mamaye jihar

- A cewar PDP, yan daban za su badda kamanni cikin kayan tsaro domin gudanar da mummunan aika-aika a yankunan Idah da Ibaji

- Ta yi zargin cewa an kwaso su ne domin su hana yan PDP kada kuri'a a ranar zabe

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ja hankalin jami’an tsaro a jihar Kogi zuwa ga zargin cewa yan daba sun mamaye ko ina gabannin zaben gwamna da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba a jihar.

Mataimakin daraktan sadarwa na PDP, Kwamrad Austin Usman Okai, ya yi zargin cewa ana sanya ran yan daban za su badda kamanni cikin kayan tsaro a Idah, “domin su gudanar da mummunan aiki akan magoya bayan PDP a zaben na ranar 16 ga watan Nuwamba.

“Wadannan jami’an tsaro na bogi sun kasance yan kungiyoyin asiri masu hatsari a gwamnatin jihar za su gudanar da aiki a tasakanin kananan hukumomin Idah da Ibaji, domin hana mambobin PDP fitowa don kada kuri’a a ranar zaben.”

Usman ya bukaci kwamadan tsaro na NSCDC da ya shiga lamarin domin hana yan daba badda kamanni a matsayin jami’an rundunar a lokacin zaben.

KU KARANTA KUMA: Manyan Fastoci sun goyi bayan koyon harshen Larabci a Najeriya

Ya yi gargadi akan makomar bari yan kungiyar asiri masu hatsari su shiga cikin jama’a, domin ana zargin za su aiwatar da mummunan aika-aika akan mutanen yankunan Idah da Ibaji.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa takarar Gwamna Yahaya Bello da mataimakinsa, Cif Edward Onoja, na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya kara samun karfi a ranar Laraba, 6 ga watan Nuwamba a Insalu, hedkwatar karamar hukumar Yagba ta gabas, yayinda tsohon mukaddashin gwamna, Cif Clarence Olafemi da daruruwan mambobin PDP a mazabar suka sanar da barinsu jam’iyyar da kuma komawasu APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel