Yan majalisa sun bukaci gwamnatin tarayya da ta bayar da N50bn don gyaran hanyoyin Neja

Yan majalisa sun bukaci gwamnatin tarayya da ta bayar da N50bn don gyaran hanyoyin Neja

- An bukaci gwamnatin tarayya da ta sama da kudade na musamman kimanin naira biliyan 50 domin gyaran hanyoyi a jihar Neja

- Yan majalisa a majalisa wakilai ne suka bukaci a bayar da kudade na musamman domin aiwatar da hakan

- A cewa yan majalisar, a kamata a samar da kudaden ga hukumar da ya kamata ta shirin cigaba na shugaban kasa

Yan majalisa na majalisar wakilai sun yi kira ga gyaran hanyoyi a jihar Neja.

A zaman majalisa na ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba, yan majalisar sun bukaci gwamnatin tarayya da ta samar da kudade na musamman na naira biliyan 50 domin gyara hanyoyi a jihar Neja.

A cewar yan majalisar, ya kamata a samar da kudaden ga hukumar da ya kamata ta shirin cigaba na Shugaban kasa.

A wani korafi da dan majalisa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sa'idu Abdullahi (Jihar Neja) ya shigar, ya ce an bayar da kwangilar wasu hanyoyi kamar su Bida-Lambata, Minna-Suleja, Tokwa-Tegina-Makera-Kaduna.

Abdullahi, a korafin wanda sauran yan majalisa takwas daga jihar Niger suka hada hannu, ya ce an bayar da kwangilar ne ga kamfanonin gine-gine daban-daban don cimma manufa.

Ya ce lokacin da aka diba domin kammala aikin gyare-gyare yya kasance sama da watanni 18 zuwa 36 kuma tuni ya dade da cika.

KU KARANTA KUMA: Yan kwanaki kafin zaben Kogi: Bello ya sake samun karfi yayinda jiga-jigan PDP suka koma APC

A cewarsa, aikin da aka yi zuwa yanzu bai wuce kaso 20 cikin dari ba tun da aka bayar da kwangilan.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Ministan aiyuka da gidaje, Babatunde Fashola, SAN, a ranar Laraba ya jaddada cewa, titunan Najeriya basu yi lalacewar da kullum ake magana a kai ba.

Yayin da yayi magana da manema labarai jim kadan bayan fitowarsa daga taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka yi ranar Laraba, yace ana zuzuta rashin kyan titunan Najeriya ne kawai.

Taron majalisar zartarwar da ya samu shugabancin mataimakin shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbajo, ya aminta da yin titunan Bida zuwa Sachi zuwa Nupeko da gadar Nupe ko zuwa Patigi da ke kan kogin Niger, wacce ta hada Nupeko da Patigi a jihohin Niger da Kwara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel