Umurnin hana kai mai iyakakokin Najeriya: Jerin garuruwa 11 da ke da kusancin 20km da iyaka

Umurnin hana kai mai iyakakokin Najeriya: Jerin garuruwa 11 da ke da kusancin 20km da iyaka

Gwamnatin tarayya ta bakin hukumar hana fasa kwabri wato Kwastam, ta bada umurnin daina sayarwa gidajen mai dake kimanin kilomita 20 da iyakokin Najeriya man fetur.

Kwantrola Janar da hukumar kwastam, Hameed Ali, ya bada umurnin ne a jawabin da wani mataimakinda Chidi, A ya fitar ranar 6 ga Nuwamba, 2019 kamar yadda Legit.ng ta gani.

Jawabin yace: " Kwantrola Janar na kwastam ya bada umurnin cewa daga yanzu kada a sake sayarwa gidajen mai da ke da kusancin kilomita 20 da iyakokinmu komin kankancinshi."

"Saboda haka a na kira ga ku dabbaka umurnin kai tsaye."

DUBA WANNAN Yanzu-yanzu: Sowore ya fara yajin cin abinci a ofishin DSS

Mun kawo muku jerin garuruwan dake kusa da iyakokin Najeriya uku da wannan abin zai shafa:

1. Gamboru Ngala - Jihar Borno

2. Mubi - Jihar Adamawa

3. Garin-gada, Yunusari LGA

4. Maigatari - Jihar Jigawa

5. Daura - Jihar Katsina

6. Jibiya - Jihar Katsina

7. Illela - Jihar Sokoto

8. Ilo, Tsamiya, Bagugu - Jihar Kebbi

9. Kamba - Jihar Kebbi

10. Idiroko - Jihar Ogun

11. Seme - Jihar Legas

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel