Yan kwanaki kafin zaben Kogi: Bello ya sake samun karfi yayinda jiga-jigan PDP suka koma APC

Yan kwanaki kafin zaben Kogi: Bello ya sake samun karfi yayinda jiga-jigan PDP suka koma APC

- Gwamna Yahaya Bello da mataimakinsa, Cif Edward Onoja, na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun kara samun karbuwa a jihar Kogi yayinda ake shirin zaben gwamna na 2019

- Hakan ya biyo bayan sauya sheka da wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da daruruwan magoya bayan jam'iyyar suka yi a jihar

- Yayinda yake tarban yan PDP da suka sauya shekar, Gwamna Bello ya basu tabbacin samun daidaito a jam’iyyar

Takarar Gwamna Yahaya Bello da mataimakinsa, Cif Edward Onoja, na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya kara samun karfi a ranar Laraba, 6 ga watan Nuwamba a Insalu, hedkwatar karamar hukumar Yagba ta gabas, yayinda tsohon mukaddashin gwamna, Cif Clarence Olafemi da daruruwan mambobin PDP a mazabar suka sanar da barinsu jam’iyyar da kuma komawasu APC.

A wajen gangamin na APC wanda aka gudanar a Insalu na mazabar Yagba, tsohon mukaddashin gwamnan kuma darakta Janar na kamfen din takarar Abubakar Ibro na gwamna a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a 2019, Cif Olafemi, tsohon kwamishinan ruwa, Osanusi, tsohon dan majalisar dokokin tarayya a mazabar Mopamuro, Eric Fiki da wasu mutane da dama duk sun koma APC.

Sauran manyan yan siyasa daga mazabar Yagba da suka bar PDP sun hada da Bola Fagbola da kuma tsohon Shugaban karamar hukumar Mopamuro, Funsho Daniyan.

KU KARANTA KUMA: Manyan Fastoci sun goyi bayan koyon harshen Larabci a Najeriya

Yayinda yake tarban yan PDP da suka sauya shekar, Gwamna Bello ya basu tabbacin samun daidaito a jam’iyyar.

A wani labarin kuma, mun ji cewa an bukaci hukumar zabe mai zaman kanta da ta dawo da Misis Natasha Akpoti ta jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a matsayin yar takara a zaben gwamna da za a yi a jihar Kogi a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Justis Folashade Ogunbanjo-Giwa ta babbar kotun tarayya Abuja ce ta bayar da umurnin a ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba.

Ta bayyana cewa INEC ta yi gaban kanta ta hanyar kin amincewa da jam’iyyar da yar takararta a zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel